Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Trump na kan gaba a sakamakon farko-farko da ya fara fito wa a zaɓen Amurka, in da ya yi wa abokiyar karawarsa Kamala fintinkau.
Zuwa yanzu Donald Trump na da kuri’un wakilan zaɓe 230 ya yin da Kamala Haris ta ke da 185, bayan Trump ya samu ƙuri’u 58,915,044 yayin da Kamala ta samu 54,753,502 daga wasu ƙuri’un da aka fara kirga wa na farko-farko.
A Jiya Talata ne miliyoyin al’ummar ƙasar Amurka su ka zaɓen shugaban ƙasar da zai kawo ƙarshen mulkin Joe Biden.
Tun da farko ƙuri’un jin ra’ayi sun nuna ana yin kankankan tsakanin tsakanin mataimakiyar shugaban ƙasar Kamala Haris da ke wa jam’iyyar Demokrat takara da kuma tsohon shugaban ƙasar Donald Trump na jam’iyyar Republican.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.