Daga Sadiq Muhammad Fagge
Shahararren ɗan kasuwar nan na Najeriya a jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata, ya ce tsarin Firaminista da wasu ‘yan majalisa ke ƙoƙarin tabbatarwa shine ne yafi alheri ga Najeriya.
Dantata, ya bayyana haka ne a lokacin da wasu ‘yan majalisar wakilai a Najeriya , ƙarƙashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, suka kai masa ziyarar neman shawara a gidansa da ke birnin Kano a ranar Alhamis.
Ya kuma bayyana godiyarsa bisa zuwan su gidansa, “ina yi wa wannan gagarumin yunƙuri naku fatan nasara”.
A cewarsa tsarin nan na Firaminista ya fi kyau ga kasar nan “saboda yana da arha sosai yayin da tsarin shugaban ƙasa mai cikakken iko yake da tsada sosai musamman ga kasa kamar Najeriya”.
“Ina fatan za ku sami haɗin kan abokan aikinku kuma ina rokon Allah ya ba ku hikima ya kuma yi muku jagora don cimma wannan kyakkyawan aiki na taimakon kasar nan”, in ji shi.
Idan za’a iya tunawa wasu yan majalisu kusan su 60 sun nuna goyon bayansu kan wannan yunƙuri na mayar da Najeriya tsarin Firaminista kamar yadda ƙasar take a jamhoriya ta farko da kuma kafin ƙasar ta sami yancin kai wanda suke ganin shine mafi sauki.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.