January 22, 2025

Tsohon Shugaban Amurka Trump Ya Tsunduma Harkar Crypto.

Tsohon shugaban kasar Amurka, Donal Trump tare da ‘ya’yan sa sun kaddamar da manhajar hada-hadar kudi ta yanar gizo da aka fi sani da cryptocurrency.

Ba a yi wani cikakken bayani ba kan tsarin crypto din da Trump, wanda shi ne dan takara shugaban kasa a jam’iyyar Republican da ahalinsa su ka samar a wani bikin kaddamarwar da aka yi na kai-tsaye tsawon awanni biyu a shafin sada zumunta.

An yi ƙaddamarwar ne kamar yadda aka tsara kuma ba a fasa ba duk da yunkurin kashe Trump da aka yi a ranar Lahadi.

Crypto: Kotu ta Aike Wa Gwamnan CBN Sammmaci Don Ya Gurfana A Gaban Ta.

Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Birnin Maiduguri.

DSS Sun Cafke Shugaban NLC Joe Ajaero.

World Liberty Financial dai tayi niyyar yin aiki ga tsarin crypto din na Trump inda za a baiwa mutane damar bada aro ko karbar aron kudin crypto wanda shafukan cryptocurrency da dama ke yi.

Dan tsohon shugaban kasar, mai suna Trump Jr. ya bayyana lamarin a matsayin “Fara juyin juya hali a fannin hada hadar kudi”, a yayin gabatarwar a shafin X.

Daily Nigerian

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *