Tumaki Kusan Dubu 16 Sun Mutu A Hanyar Saudiyya, Yayin Da Miliyoyin Musulmi Zasu Yi Layya A Ƙasar.

Tumaki
Page Visited: 1207
0 0
Read Time:36 Second

Rahotanni daga Sudan na cewa, hukumomi a ƙasar sun ce dubban tumaki sun mutu a ruwa bayan wani jirgin ruwa ya kife a hanyarsa ta zuwa ƙasar Saudiyya.

Wannan na zuwa ne yayin da ƙasar ke karɓar baƙuncin musulmi daga ƙasashen duniya domin yin aikin hajin bana.

Jirgin da ya kife dai na ɗauke da kusan dabbobi dubu 16, dama bil’adama.

Rahotanni sun ce duk bil’adaman da suke cikin jirgin sun tsira da rayukansu, tumakin ne kawai suka mutu.

Jami’an tashar ruwa a Sudan ɗin sun bayyana cewa adadin dabbobin da jirgin ya kwasa ya fi ƙarfin adadin da zai iya ɗauka.

Miliyoyin musulmi ne ke shirin yi layya a ƙasar Saudiyya, wanda hakan ka iya sa buƙatar tumakin ta ƙaru.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Matashi Ya Yiwa Mahaifin Budurwarsa Mummunan Rauni Bayan Ya Hana Shi Kaiwa Dare Idan Yaje Zance.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Saurayin ya yiwa mahaifin budurwarsa rauni ne bayan da baban budurwar tasa ya hana shi kaiwa dare idan yaje zance a garin Ɗan Hassan, da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Arewa Radio ta rawaito cewa, an jiwa mahaifin budurwar raunine bayan da ya umarce saurayin […]

Read More
Labarai

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata. Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau. Haka nan sun […]

Read More
Labarai

Lauyan Gwamnatin Kano Ya Nemi Kotu Ta Yiwa Abduljabbar Hukunci.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci. Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari’ar sun gabatar da Jawabansu na karshe […]

Read More