April 1, 2025

Wani bawan Allah a jihar Zamfara ya rage farashin kayan abinci saboda zuwan Azumi.

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Wani mai aikin tawali’u Alh. Rabi’u Bello Najanun Kaura Namoda dake jahar Zamfara, ya sauƙaƙa kayan abinci ga al’ummar yankin shi, domin samun sauƙi a cikin watan Ramadan.

A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, Alh. Rabi’u Maigidaje ya ce fitar da kayan ne daga cikin kayan da ya noma in da ya kara sawo wasu kasuwa ya haɗa, domin sayarwa ga masu buƙata cikin farashi mai sauki.

Yana sayar da Gero akan naira 1600, Dawa 1450, Masara 1450.

A wasu sassa na Gusau da Kaura Namoda wasu suna sayar da gero daga naira 1700 zuwa 1800, ana sayar da masara daga naira 1500 zuwa 1600, hakama ana sayar da Masara akan 1500 zuwa 1600.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *