January 22, 2025

Wani matashi ya kashe Mahaifiyarsa akan abinci a Akwa Ibom

 

Wani matashi dan shekara 23 mai suna Akaninyene Sunday Isaac, ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 55, Christiana Sunday Isaac saboda abinci.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, matashin dan asalin kauyen Oruk Uso Otoro da ke Karamar Hukumar Abak ya kashe mahaifiyarsa har lahira saboda zargin ta hana shi abinci na tsawon kwanaki uku.

‘Yan uwan wadanda abin da ya shafa sun shaida wa wakilinmu da ke Uyo cewa, Isaac yakan nemi kudi daga wajen mahaifiyarsa wadda a kullum take biyan bukatarsa, amma a wannan ranar ta ki amincewa da bukatarsa, inda ta ce ba ta da kudi.

An ruwaito cewa, rashin ba shi kudin ne ya harzuka matashin wanda ya yi amfani da adda ya sassari mahaifiyarsa, lamarin da ya kai ga rasuwar ta kafin a karasa asibiti.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Odiko Macdon, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce matashin ya shiga hannu tun a ranar 11 ga watan Oktoba kuma za su mika shi gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *