March 11, 2025

Wani mummunan hatsarin mota ya kashe 38 wasu 39 sun jikkata a Bolivia.

Aƙalla mutum 37 sun rasa rayukan su, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku tsakanin manyan motoci biyu a yankin Potosi da ke yammacin Bolivia, in ji ‘yan sanda da mahukunta.

Al Jazeera ta ruwaito cewa hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 7 na safe agogon gida, (11:00 GMT) a ranar Asabar a kan hanyar da ke tsakanin garuruwan Uyuni da Colchani, lokacin da ɗaya daga cikin motocin ta kauce daga hanya ta shiga hanyar wata mota da ke tahowa.

“Wannan mummunan hatsari ya jawo mutuwar mutum 37, sannan muna da mutum 39 da suka jikkata dake kwance a asibitoci huɗu da ke garin Uyuni,” in ji mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan yankin Potosi.

‘Yan sanda sun ce suna aiki don gano sunayen waɗanda suka mutu da kuma waɗanda aka kwantar a asibiti.

Daya daga cikin motocin tana kan hanyar zuwa Oruro, inda ake gudanar da wani babban buki na Latin Amurka a wannan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *