Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wasu da ake zargin masu satar shanu ne sun hallaka fiye da mutane goma, ciki har da ‘yan sa-kai a kauyen Mansur da ke yankin Gwana, ƙaramar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kuma sace shanu da tumaki daga Mansur da wasu ƙauyuka da ke makwabtaka da shi, yayin da suka kai hari cikin dare.
Majiyoyi sun bayyana wa LEADERSHIP cewa ‘yan sa-kai sun gamu da ajali ne a cikin kwantan bauna yayin da suke sintiri.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 4 ga Mayu, 2025 da misalin ƙarfe 9:40 na safe.
Wakil ya ce an samu rahoton ne daga ofishin ‘yan sanda na Alkaleri, inda aka bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka wa wata tawagar masu sintiri da ke yawo tsakanin yankunan Duguri, Mansur da dajin Madam da ke iyakar Bauchi da Filato.
> “Wannan hari ya janyo asarar rayuka da dama daga bangarorin biyu – na ‘yan sa-kai da kuma ‘yan bindigar da suka kai harin,” in ji sanarwar ‘yan sanda.
Ya ce an aika da ƙungiyoyin sintirin musamman zuwa wurin da harin ya faru, inda suka gano gawarwakin waɗanda suka rasa rayukansu.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da ‘yan sa-kai da kuma fararen hula daga kauyen Sabuwar Sara, waɗanda suka sha da ƙyar wajen tserewa daga harin kafin a bindige su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Sani Aliyu, ya kai ziyara zuwa wurin da harin ya auku domin duba halin da al’umma ke ciki da kuma jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa.
LEADERSHIP ta tuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka kai irin wannan hari a Mansur da wasu ƙauyuka makwabta ba, inda aka sha kashe mutane da ƙone gidaje a lokutan baya.