Daga Abdul’aziz Abdullahi
Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kashe wani basaraken gargajiya mai matsayin Hakimi tare da ƙona gidaje da sace dabbobi da ba a san adadinsu ba a ƙaramar Hukumar Billiri ta jihar Gombe.
Maharan da ake zargin makiyaya ne sun kutsa garin Powishi da ke yankin Kalmai ne a cikin dare in da su ka kashe Hakimin, Malam Yusuf Akwara, sannan su ka ci gaba da yin aika-aika.
Da ya ke tabbatar da kai harin, kakakin Ƴansandan jihar Gombe ASP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne a kan babura a daren Laraba, in da suka tayar da tarzoma.
An yi arangama tsakanin makiyaya da manoma a jihar Gombe.
Babban hafsan Sojin ƙasa ya sha alwashin kawo ƙarshen Ƴan ta’addan Lakurawa cikin kankanin lokaci.
A safiyar Alhamis, DPO na ƙaramar hukumar Ɓilliri ya sanar da rundunar game da harin, in da ta tura tawagar jami’an tsaro hadin gwiwa ta ’yan sanda da sojoji zuwa wajen domin shawo kan lamarin.
Sai dai kuma, maharan sun tsere kafin isowar jami’an tsaro, amma duk da haka, mazauna yankin da jami’an tsaro sun yi nasarar kashe wutar da maharan suka banka wa gidajen.
Kwamishinan ’yan sanda jihar, Hayatu Usman tare da kwamandan rundunar soji ta 301 da kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC da shugabar ƙaramar hukumar Ɓilliri, sun kai ziyara kauyen don duba barnar da aka yi.
Sun kuma yi ta’aziyya ga Mai Tangale Hakimin Kalmai da iyalan wadanda abin ya shafa, tare da al’ummar yankin.
Sanarwar ta ce rundunar ta tura tawagar bincike domin kamo waɗanda suvka yi wannan ɗanyen aiki, ta na mai kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu tare da ba jami’anta haɗin kai a binciken da suke gudanarwa, yana tabbatar da cewa za a hukunta masu wannan aika-aika.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP