Wata kungiya mai suna Neutral Minds for Nigeria’s Political Growth and Development, ta buƙaci Gwamnatin Jihar Zamfara da ta kama daya daga cikin jagororin jam’iyyar APC Sani Abdullahi Shinkafi, bisa zargin karya dokar hana tarukkan siyasa a jihar.
Sai dai yayin da aka tuntube shi domin jin ta bakin sa kan wannan zargi, Shinkafi ya musanta cewa ya saɓa dokar gwamnatin jihar, ya na mai cewa babu wata takardar doka da ta hana tarukan siyasa a Zamfara.
Tun a watan Fabrairu 2025, Gwamna Dauda Lawal ya fitar da wata sanarwa ta hannun mataimakin sa na musamman kan kafafen watsa labarai Mustapha Jafaru Kaura, in da ya sanar da hana duk wasu harkokin siyasa a faɗin jihar domin shawo kan matsalar tsaro da ke kara taɓarɓarewa.
An dauki wannan mataki ne bayan taɓarɓarewar tsaro a ƙaramar hukumar mulkin Maru, lamarin da ya kara tayar da hankulla a jihar.
Shugaban Neutral Minds for Nigeria’s Political Growth and Development Obed Bawa, ya zargi Shinkafi da ƙaddamar da wata ƙungiyar sa ta siyasa a ranar 5 ga watan Fabrairu 2025, a gidansa da ke Gusau.
Bawa ya ce: “Mu na kira ga gwamnatin jihar Zamfara da hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakin da ya dace, ta hanyar kama Sani Abdullahi Wamban Shinkafi wanda ya karya doka a ranar 5 ga watan Fabrairu 2025, ta hanyar ƙaddamar da wata ƙungiyar sa mai suna ‘Wamban Shinkafi Democratic Fronts’ a gidan sa da ke Gusau.”
“Kaddamar da wannan kungiya a makon da ya gabata ya sabawa umarnin gwamnati, kuma hakan ya kara tayar da hankula a jihar Zamfara.”
Bawa ya ƙara da cewa Shinkafi ya yi suka kan jam’iyyar APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin taron da kuma a wata tattaunawa da ‘yan jarida daga baya, abin da ke iya haddasa rashin kwanciyar hankali a jihar.
“A taron, Sani Abdullahi ya bayyana aniyar sa ta yin takarar gwamnan Zamfara a shekarar 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, wanda hakan na zuwa a lokacin da bai dace ba kuma ya na iya haifar da ruɗani a jihar.”
“Wannan jigo na APC wanda tsohon sakataren jam’iyyar APGA ne, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna bambanci wajen naɗe-naɗe, har ma ya bayyana cewa shugaban kasa ya kamata ya bai wa ‘yan siyasar Zamfara hakuri saboda gazawar sa wajen nada mambobin jam’iyyar a mukaman gwamnati.”
Sai dai, yayin da yake mayar da martani Shinkafi ya shaida wa jaridar Leadership cewa, taron da aka ce ya gudana ba taron siyasa ba ne, illa kawai taron ƙungiyar sa ne wanda aka yi a gidan sa, don haka ba zai iya zama barazana ga tsaro a jihar ba.
Kan batun sukar Tinubu, Shinkafi ya ce ya na nan daram kan maganar sa cewa Zamfara ba ta sami sakamako na siyasa ba, duk da gudunmawar da ta bayar wajen samun nasarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotu ta bayar da umarnin karɓe dalar Amurka miliyan 1.4 daga Emefiele
-
“Noma shi ne ginshikin rayuwa, domin babu rayuwa ba tare da abinci ba”-Barau.
-
Kutu ta ɗaure likitan bogi da ya yi shekaru 10 ya na aiki a Abuja.
-
Tsadar Rayuwa: Ba Da Daɗewa Ba Abubuwa Za Su Yi Kyau -Gwamnatin Najeriya.
-
Ƴan Kasuwar Man Fetur Sun Fara Siyen Man Daga Matatar Dangote.