Rahotanni daga Ibadan babban birnin jihar Oyo na cewa, wata tankar dakon man fetur ta yi bindiga bayan da ta yi taho-mu-gama da wasu manyan motoci biyu.
Aminiya ta rawaito, faɗuwar tankar man ke da wuya ta kama da wuta, in da daga bisani ta yi bindiga ta ƙone direbanta ƙurmus har lahira a cikinta.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2.30 na dare, bayan tankar ta ƙwace a hannun direbanta ta yi karo da wasu manyan motoci biyu sannan ya yi adungure, a yankin Fijabi da ke Babbar Hanyar Ojoo zuwa Iwo a ranar Laraba.
Darakta Janar na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo, Yemi Akinyinka, bayyana cewa “direban tankar man fetur ɗin ya rasu, yaron motar guda ɗaya kuma ya samu rauni ana kula da shi a Asibitin Koyarwar na Jami’ar Ibadan.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Dokin rundunar Sojin Najeriya mai muƙamin Sajan ya mutu a Kaduna.
-
Ɓarawo ya mutu yayin da ya ke ƙoƙarin sata a cikin Taransifoma.
-
Yansadan jihar Adamawa sun fara bincike kan wasu mutum 2 da zargin sun yi wa yara mata biyu Fyade.
-
Yayin da Ƴansandan Kano su ka gargaɗi al’umma kan shiga cunkoso saboda barazanar tsaro gwamnatin jihar ta ce taron Mauludin Shehu Inyass ya na nan daram.
-
Gwamnatin Sokoto ta gargaɗi al’umma kan kwararar ƴan bindiga jihar.