Daga Muhammad Fatihu Maisikeli
Godiya ta tabbata ga Allah tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w
Haƙiƙa aure bauta ce, ko na ce ibada ce ga dukkanin ɓangarori biyu (Mata da miji)
Amma a bangaren mata suna ganin kamar wani waje ne na holewa da sakewa, haka ne matuƙar an gina auren akan gaskiya da amana.
Amma ya kamata iyaye musamman mata su dinga sanar da ƴaƴansu cewa sai an yi haƙuri da juriya kafin a sami wannan nasara da holewa.
Hakan zai rage samun zawarawa da matan da suke wuce lokacin aure ba tare da sun sami tsayayyen mijin ba.
Hakan kuma zai sake rage yawaitar ayyukan ɓarna wanda addini ya yi hani da su.