December 2, 2021

Yakamata A Tausayawa Al’umma Saboda Halin Da Suke Ciki Na Matsi – Koli.

Page Visited: 343
0 0
Read Time:1 Minute, 5 Second

Daga Muhammad Sani Abdulhamid

Kungiyar zauren hadin kan al’ummar jihar Bauchi da cigaban jihar, ta  yi taronta na shekara kamar yadda ta saba a ko wacce shekara.

Da yake bayyana makasudin shirya taron a wannan shekara bayan tashi daga taron shugaban kungiyar kwamared Abdullahi Koli, ya ce, “taron bita ne na shakara guda da kuma yin la’akari da al’amura yadda suka kasance a jihar Bauchi da fadin kasa, mun bada karfi a kan harkar siyasar taltalin arziki da zamantakewar al’umma”.

Koli Ya kuma ce, “akwai al’amuran da yakamata a tausayawa talaka saboda halin da al’umma ke ciki na matsi da taltalin arziki da halin zamantakewa na rashin tsaro”.

Hon. Musa Muhammad, da ya fito daga karamar hukumar Kirfi, ya bayyana gamsuwar sa da yadda taron ya gunada wanda ya ce, domin abunda kungiyar ke so ta kawowa al’ummar jihar Bauchi shine “ta jawo hankalin mutane kan hadin kai a zama tsintsiya maurinki daya, a gaskiya kungiyar tana kokari sosai yakamata a yayata ayyukan kungiyar domin t ratsa ko ina a jihar Bauchi”.

Kazalika a gurin taron sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha kan lallai-lallai ta yi azama taga cewar ta taimakawa talakawa da mafita musamman tsaro da abinci.

Taron dai ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki birnin Bauchi da kewaye.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *