August 8, 2022

Yakamata Atiku Ya Jawo Mahiru Domin Cin Zabe Cikin Sauki A Bauchi.

Page Visited: 574
0 0
Read Time:1 Minute, 7 Second

Daga: Mai Gari

Duba kwarewar Mahiru Maiwada Wundi, wajen yafiyaar da harkar siyasa musamman bangare tuntuba tun daga mazaba da anan ne ake cin zabe, zai kyu ace tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasaa jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, akwai shi a ciki domin ya jagoranci shiga lungu da sakon jihar Bauchi don tabbatar da nasarar Atiku.

Mahiru Maiwada, goggene ta fuskar aikin gwamnati da iya mu`ala wanda anga hakan a lokacin da ya yi kwamishina har sau biyu a jihar Bauchi.

Maiwada wanda ya dade yana yiwa al`umma hidima da kudaden al`jihunsa idan aka bashi irin wannan damar zai jawowa wannan tafiya ta Atiku daraja da karfuwa a jihar Bauchi, idan ahar ana son ayi nasara ya zama wajebi a jawo shi jika, domin mutum ne mai farin jini da karbuwa a gun jama`a.

Mahiru yana da ala`ka mai kyau da matasa da mata da dattawa saboda irin ayyukansa na jinkai garesu wadannan rukukun mutane sune ake cin zabe da su, saboda sune masu yin zabe, ba shakka suna jin maganar sa.

Muna bawa ɗan takarar shugaban ƙasaa jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, shawara bashi ko`odinatan yakin neman zabe na jihar Bauchi, insha Allahu zai fita kunya, ka zalika muna bawa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, shawara ayi duk wata tafiya da Mahiru Mai Wada Wundi, don samun nasara.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *