August 8, 2022

`Yan Bindigar Da Suka Sace Dalibai A Kaduna Na Neman Taimakon Abincin Da Za Su Ciyar Da Daliban.

Page Visited: 202
0 0
Read Time:1 Minute, 8 Second

Yan bindigar da suka sace daliban makarantar sakandaren Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sama da 120 sun bukaci taimakon abinci domin ciyar da su, inda suke cewa basu da abincin da zasu basu.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa mataimakin shugaban makarantar ta Bethel Baptist High School Wakili Madugu ya bayyana cewar Yan bindigar sun tintibe su inda suka tabbatar musu da cewar dalibai 121 ke hannun su daga cikin daliban da suka kwashe ranar litinin.

Madugu yace yayin tattaunawar da suka yi da su ta waya Yan bindigar sun shaida musu cewar basu da abincin da zasu ciyar da daliban, saboda haka suna bukatar akai musu shinkafa ‘yar waje buhu 10 da ‘yar gida buhu 20 da wake buhu 20 da gishiri buhu 2 da katon 10 na man girki da maggi katon 10 domin ciyar da su.

Wakili Madugu mataimakin shugaban makarantar Bethel Baptist da ‘yan bindiga suka sacewa dalibai 121

Mataimakin shugaban makarantar yace suna tattaunawa da jami’an tsaro domin daukar matakin da ya kamata na kare lafiyar daliban da kuma kubutar da su cikin ruwan sanyi.

‘Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS. AP – Sunday Alamba
Madugu wanda yace ya zuwa yanzu Yan bindigar basu bayyana kudin da suke so a basu a matsayin kudin fansa ba, yace sau biyu suke tintibar su a ranakun litinin da talata.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *