January 22, 2025
CP Gumel

Creadit/Kiyawa

Yan Sanda A Kano Sun Dauki Matakan Tsaro Gabanin Yanken Hukuncin Kotu Kan Zaben Gwamnan Jihar.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce ta dauki dukkan matakan tsaro da suka zama dole a muhimman wurare don tabbatar da tsaron rayuka da kuma dukiyar al’umma, gabanin hukuncin da kotun daukaka kara za ta yanke a kan zaben gwamnan jihar.

Cikin wata sanawar da rundunar yan sandan ta fitar mai dauke da sa hannun Kakakinta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ranar Litinin, ta ce jami’ansu da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro da ke aiki a Kano sun tura isassun ma’aikata da kayan aiki zuwa wasu muhimman wuraren da suka tantance a jihar.

Rundunar ta kuma yi kira ga al’ummar jihar Kano su guji shigar da kansu cikin duk wani abu da zai kai ga karya doka.

BBC Hausa, ta ce, matakin mai yiwuwa na nuna cewa ranar sanar da hukuncin kan wannan shari’a ta gabato, ko da yake har yanzu, kotun ba ta fitar da bayani a kan ranar yin hakan ba a bainar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *