March 12, 2025

Yansandan Abuja sun yi ajalin sama da mutum 15 cikin su da masu garkuwa da mutane.

Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja sun hallaka mutane bakwai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, da kuma 9 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a cikin watanni biyu da suka gabata.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an ‘yan sanda sun kama mutane dari uku, tare da kwato makamai da harsasai masu yawa, da kuma miyagun kwayoyi daga ranar ɗaya ga watan Janairu zuwa 28 ga watan Fabrairu 2025.

Da yake jawabi kan lamarin, Kwamishinan ‘Yan Sandan babban birnin tarayya CP Olatunji Disu, ya bayyana cewa an tura tawaga ta musamman ne domin kai farmaki a wuraren da ake zargin maboyar masu laifi ne a Abuja.

CP Disu ya ce Dei-Dei, Karu, Gwarinpa, Jikwoyi, Karimo, da Maitama na daga cikin wuraren da aka kaddamar da farmakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *