Rundunar ‘yan sandan jihar Lagas ta fallasa tare da rushe wata haramtacciyar cibiyar koyar da damfara ta intanet, wadda aka fi sani da “Makarantar Yahoo,” a yankin Iju na jihar.
Kakakin rundunar Benjamin Hundeyin, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya bayyana cewa an kama manyan wadanda ake zargi su hudu tare da dalibai guda shidda.
A cewar sa, daya daga cikin dalibban da aka kama karamin yaro ne mai suna Minachi Udochukwu.
Hundeyin ya bayyana cewa bincike na farko ya nuna cewa shugabannin makarantar sun dauko matasa daga jihar Anambra, suna koyar da su damfara ta intanet, sannan suna kwace kudaden da suka samu.
Sanarwar ta kara da cewa, “A yayin nasarar da aka samu, jami’an ‘yan sanda sun kama kwararrun masu damfara hudu da ke gudanar da wannan makaranta ta damfara. Wadanda aka kama su ne Chibuike Ihejika mai shekaru 23; Stanley Ihejika ɗan shekara 22; Obiora Oyediba mai shekara 26; da Emmanuel Oyedibe mai shekra 25.
“Sauran mutane guda shidda da aka kama daliban su ne, wadanda ke karbar horo kan damfara ta intanet, Sun hada da Okorie Henry, Otoh Chisom mai shekaru 20; Okeke Kwufrochikwu dan shekara 26; Uchenna Obeji dan shekara 26; Minachi Udochukwu mai shekaru 12; da Chinedu Ukachukwu mai shekaru 23.
“Kudaden da suke samu daga damfarar da suke yi, shugabannin makarantar ne ke kwace su.”
Rundunar ta gargadi mai mallakar makarantar da ya mika kansa ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar. Haka kuma, rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da duk waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala bincike.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP
-
Babu wani gurbi a gidan gwamnatin Delta cewar Dennis Guwor ga ƴan takarar gwamnan jihar.