March 11, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Yansandan jihar Nasarawa sun kama wani ɗan fashi da amfani da kayan sojoji wajen aikata laifuka.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ta kama wani mamba na kungiyar fashi da makami da ke aikata laifuka sanye da kakin soja, a kan titin Abuja zuwa Keffi da wasu yankuna na Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Lafia, in da ya ce jami’an ‘yan sanda daga ofishin Angwan Lambu da ke Keffi, sune suka cafke wanda ake zargin bayan samun sahihan bayanai na sirri.

Ya ce wanda ake zargin mai suna Godswill Achili, an kama shi ne ya na sanye da kakin soja.

Bayanin ya nuna cewa “Bayan bincike, ya amsa da cewa ya na aikata fashi da makami in da ya ke kwaikwayon soja.”

Bincike ya nuna cewa Achili mamba ne na wata kungiyar masu aikata laifuka, da ke fashi da makami a yankunan babban birnin tarayya Abuja da kuma Nasarawa” in ji shi.

Mambobin ƙungiyar na sanya cikakken kakin soja yayin aikata laifukka, suna amfani da bakar mota kirar Toyota Avalon, suna mayar da hankalin su ga matasa da ɗalibbai da ke tafiya tsakanin Keffi, New Karu, da kuma Abuja.

Suna yaudarar mutane su shiga motar su, sannan su kwace musu kayayyaki kamar kudi da wayoyi.

SP Nansel ya ƙara da cewa akwai wasu mutum biyu na kungiyar da suka gudu, kuma rundunar ‘yan sanda tana kan kokarin kamo su.

“Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Nasarawa CP Shetima Jauro Mohammed, ya bukaci jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wata bakuwar ijiya dake nuna alamun aikata laifi don dakile miyagun ayukka a jihar,” in ji Kakakin Rundunar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *