Rundunar Ƴansandan jihar Neja ta kama jami’in da harbin sa ya samu wani ma’aikacin shige da fice bisa kuskure, yayin da ake kokarin tarwatsa ‘yan daba a Minna, jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Mataimakin Sufuritandan Shige da Fice (ASI) Christian Oladimeji, ya samu raunin harbin bindiga bayan wata tawagar ‘yan sanda da ke sintiri, ta fuskanci hari daga ‘yan daba yayin da suke kokarin kwato wasu kayayyakin da ake zargin an sato su ne.

Yayin da yake mika tallafin naira miliyan daya ga iyalan wanda aka ji wa rauni domin taimakawa wajen neman magani, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Neja Shawulu Ebenezer Danmamman, ya bayyana cewa jami’in da ya harba bindigar an kama shi, kuma yana fuskantar hukunci na cikin gida tare da sauran jami’an da ke aiki da shi a lokacin da lamarin ya faru.

A cewar wata sanarwa da Kakakin Rundunar SP Wasiu Abiodun ya fitar, ta ce mataimakin kwamishinan yan sanda mai kula da harkokin mulki Aminu Garba ne ya wakilci CP Danmamman a lokaci mika kudin.

Kwamishinan ya nuna godiya ga iyalan wanda aka ji wa rauni saboda hakuri, kulawa da goyon bayan su, tare da tabbatar musu da cewa rundunar za ta ci gaba da tuntubar su har zuwa lokacin da za a kammala jinyar sa.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *