March 11, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Yansandan jihar Zamfara sun miƙa cakin kuɗi ga iyalan jami’an su da suka rasu a bakin aiki

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta mika takardun ceki na kudi har N94,555,327.69, ga iyalan jami’an ‘yan sanda 23 da suka rasu yayin gudanar da ayyukan su.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Muhammad Shehu Dalijan, shine ya mika chekin a madadin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun, a wajen wani biki da aka gudanar a Gusau.

Ya bayyana cewa ko da yake kudin ba zai iya maye gurbin ‘yan uwan su da suka rasu ba, an bayar da shi ne domin tallafa masu a wannan lokaci mai wahala. Haka kuma, ya shawarce su da su yi amfani da kudin ta hanyoyin da za su amfanar da su a nan gaba.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin ya nuna godiya ga shugabancin ‘yan sanda bisa wannan taimako, tare da yin addu’a domin kariya ga dukkan jami’an ‘yan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *