Daga Fatima Suleiman Shu’aibu.
Rundunar Ƴansandan Kano a Najeriya, ta ce ta samu nasarar kama wani matashi mai suna Saifullahi Abba ɗan shekara 23 mazaunin unguwar Kofar Fada a garin Wudil da ke jihar da zargin laifin sace wata karamar yarinya ‘yar shekara 4 ya yi garkuwa da ita.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da sace yarinyar mai suna Nabila, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya kuma wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewar sanarwar tun farko mahaifin yarinyar mai suna Zulkiflu Abdullahi mazaunin ƙauyen Dakatsalle da ke yankin ƙaramar hukumar Bebeji shi ne ya shigar da ƙorafi ofishin Ƴansanda kan cewa, an sace ƴarsa mai shekara 4 sannan waɗanda su ka sace ta sun kirashi sun buƙaci ya ba su kuɗin fansa Naira miliyan 3.
Matashi Ya Kashe Kansa Sanadin Sauraron Kiɗan Gangi A Kano.
An gano shinkafar da Tinubu ya bayar a raba ana canza musu buhu a Kano.
Ƴarsanda ta yi barazanar kashe kanta da ƴaƴanta.
Kiyawa ya kuma ce, bayan bincike da rundunar ta yi ta samu nasarar kama Saifullahi Abba a ƙauyen Luran da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, in da daga nan ne ya kai su in da ya ɓoye yarinyar kuma tuni Ƴansanda sun ceto yarinyar har sun kaita asibiti an duba lafiyarta, kalau take.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
“Kwararar masu aikata laifuka daga jihohin makwabta ne abin da ya taimaka wajen ƙalubalen tsaro”- Gwamnatin Gombe.
-
Kano da Katsina, sun zama a sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kuɗi.
-
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
-
Ƙungiyar Alkalai sun shiga yajin aikin sai baba ta gani.
-
NAFDAC ta gargaɗi masu gidajen Burodi kan amfani da Sakarin.