Kungiyar da ke Yaki da Kwacen Waya a Jihar Kano ta Youth Against Phone Snatching YAPS ta roƙi gwamnan jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ya Samar da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida Ministry of Defence and Internal Affairs.
Ta bukaci hakan ne a gun gwamnati bayan da ta ce ta yi nazari kan hakan,”kungiyar ta yi nazari mai zurfi wajen binciken yadda matsalar tsaro take sake ƙamari a jihar Kano musamman ma daga matakin farko wato cikin al’umma,” a cewar shugaban ƙungiyar Abdulwahab Said Ahmad.
Wannan dai na ƙunshene cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar ta fitar, inda sanarwar ta ƙara da cewar, Idan an samar da ma’aikatar zata janyo dukkan ƙungiyoyin tsaro da ke yin aikin sa kai domin basu bita da kuma yi musu jagora wajen gudanar da ayyukansu.
“Idan akayi nazari sosai yanzu, ƙungiyoyin da ake dasu na tsaro sun fi na da yawa amma kuma duk da suna iya bakin ƙoƙarinsu ayyukan naso su fi ƙarfinsu, hakan na da alaƙa da rashin sanin makamar aikin da kuma goyan baya na al’umma da gwamnati,” inji Abdulwahab.
Shugaban ƙungiyar ya ce sun gano ƴan Vigilatte da ƴan sandan kwansabulare suna aiki ne dai dai da tinanin ba tare da kwarewa ba.
“Wani bincike da mukai akan Vigilatte da ƴan sanda sarauniya (Special Constabulary) mun gano cewa Yan Vigilatte na yin aikin su ne dede da tunaninsu basu sanin iyakar su bare inda za su tsaya, gashi kuma al’umma basa taimaka musu bare gwamnati, kuma da ba dan su ba, da babu unguwar da za a iya bacci a yanzu.”
“Special Constabulary” sunfi Regular yan sanda yawa a kowanne Out post kuma su suke kame amma babu bani tsari da suke kai wanda za su sami abun batarwa domin CI da Iyali Hakan Yana Kawo nakasu a aikin.”
Wannan dai na zuwa ne yayin da ayyukan kwacen waya da faɗan daba ke ƙara ta’azzara a jihar, sai da kuma hukumomi na cewa na kawo karshen ayyukan kwacen waya da faɗan daba.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Har yanzu ina matuƙar son Buhari, in ji fasinjan da ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga.
-
Hana Acaɓa A Jihar Bauchi: Abubawan Da Ake Musu Gaskiya Ba Da Hannun Gwamnatin jihar Bauchi Bane, -Gwanma Bala.
-
KAROTA Ta Kama Wani Matashi Da Ke Sojan Gona Da Sunanta.
-
Gwamnatin Kano Ta Yiwa Sheikh Qaribullahi Kabara Kyautar Fili.
-
Kungiyar Mawakan Sahwa Da Aka Yaɗa Mutuwar Su Sama Shekaru Goma Za Su Gana Da Ƴan Najeriya Ranar Asabar.