Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Gwamnan jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad, zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 ga majalisar dokokin jihar a Yau Alhamis.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan Mukhtar M Giɗaɗo, wadda ya fitar a ranar Laraba a birnin Bauchi.
Sanarwar ta ce, miƙa kasafin kuɗin ya biyo bayan kudirin da majalisar zartarwar jihar ta yi ne kan kasafin kuɗin na shekarar 2025 a ranar Laraba 20 ga watan Nuwamba.
Gwamnan Bauchi Ya Buƙaci Gwamnatin Najeriya Ta Saki Yaran Arewa Da Take Tsare Da Su A Abuja.
Gidauniyar OVPCF Ta Tube Shugabanta Na Bauchi, Tare Da Sallamarsa Baki Ɗaya.
Ana ana sa ran Gwamnan zai miƙa kasafin kuɗin ne da misalin ƙarfe 10 na Safiyar wannan rana.