February 23, 2025

Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wasu rahotanni da ke fitowa na cewa, asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya ga motocin kayayyakin agaji da dama da suka kaasance a ajiye a Jordan, in da suke shirin shiga domin isar da kayayyakin zuwa Gaza.

Kakakin asusun, Rosalia Bollen ta shaida wa BBC cewa suna fata hanyoyin da aka bi, za su taimaka wajen tsagaita wuta a yankin.

Sai dai ta ce ko da ma an shigar da kayayyakin, raba su zai yi wahalar gaske, “saboda yadda yankin ya ɗaiɗaice.”

Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.

Wani Babban Kwamandan Sojin Isra’ila Ya Baƙunci Lahira A Gaza.

A Safiyar Juma’ar An Kashe Mutum 109 A Gaza Bayan Ƙarewar Wa’adin Tsagaita Wuta.

A ranar Larabar da ta gabata ne aka cimma matsaya kan yarjejeniyar zaman lafiya na dindindin a Gaza da kuma sakin waɗanda Hamas ke garkuwa da su gami da sakin fursunonin da Isara’ila ta kama a ranar Lahadi mai zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *