Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Za a sake zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Rivers bayan kotun Koli ta rushe wanda aka yi a shekarar da ta gabata. - Martaba FM Za a sake zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Rivers bayan kotun Koli ta rushe wanda aka yi a shekarar da ta gabata. - Martaba FM

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa za ta yi aiki da hukuncin kotun ƙolin ƙasar, bayan ta yi cikakken nazarin takardun hukuncin.

BBC ta rawaito, yayin wani jawabi da ya gabatar wa ƴan jihar a ranar Lahadi, Mista Fubara ya ce gwamnatinsa za ta bai wa hukumar zaɓen jihar haɗin kai wajen sake shirya wani zaɓen ƙananan hukumomin, bayan kotun ta rushe wanda aka yi a shekarar da ta gabata

A ranar Juma’a kotun ƙolin ƙasar ta rushe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar 5 ga watan Oktoban 2024.

Gwamnan ya kuma umarci duka shugabbanin ƙananan hukumomin su miƙa ragamar gudanar da ƙananan hukumomin ga daraktocin mulki na ƙananan hukukomin a gobe Litinin 3 ga wata.

Ya kuma bayayna aniyar naɗa shugabannin riƙo har zuwa lokacin da za a sake gudanar da wani sabon zaɓen.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *