December 2, 2021

Zuwan Buhari Kano Akwai Tarin Alkairai Cikin Aikin Titin Jirgin Kasa Daya Kaddamar.

Page Visited: 146
0 0
Read Time:1 Minute, 19 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

A ranar Alhamis shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kano domin kaddamar da fara aikin titin jirgin kasa da zai tashi da jihar zuwa jihar Kaduna da kuma bude wasu ayyuka wadanda gwamnatin jihar Kano ta yi.

Babu shakka wannan aiki titin jirgin kasa akwai tarin alkairai da yawa cikin sa idan har aka kammala kasancewar jihar Kano jiha ce da tayi fice wajen kasuwanci.

Yin wannan aiki zai taimakawa yan kasuwa wajen shige da ficewa wanda ita daman harkar sifiri tana daga cikin jigo wajen kasuwanci.

Mutanen Kano suna fita waken jihar sayo kaya sosai haka na ana shigawa daga wasu jihohi sosai zuwa jihar saboda titin zai saukake komai tare da sanya kwanciyar hankali ga zukatan yan kasuwa kuma zai taimaka wajen samar da aikin a jihar dama makwabtakan jihar.

Hakika za a kara samun bunkasar talatin arziki mai yawa gami da samuwar abinci da daman irin ayyakan da yakamata tun zuwa gwamnati ta mayar da hankali kai.

Yanzu ya ragewa yan majalisun tarayya da suka fito daga jihar Kano su mayar da hankali wajen sanya ido don ganin an kammala aikin a garen lokaci, ba tare da jan ciki ba.

Ita kanta gwamanatin sai ta dage sosai wajen ganin ta sauke wannan nauyi da ta dauka na kaddamar da fara wannan aiki tare da ganin ta kawo karshen sa kafin karewar wa’adinta.

Mu muku yan jihar Kano abunda yakamata muyi shine mu taya gwamnatin da addu’a don neman Allah taimaka musu su kare wannan aiki a kan lokaci saboda irin mahimmancins a ga jihar da al’ummarta.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *