Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, al’ummomin wasu garuruwa shida na yankin ƙaramar hukumar Danmusa, sun ce suna cikin halin ƙaƙa-nika-yi, sakamakon harajin naira miliyan goma da ƴan bindiga suka ƙaƙaba masu, baya ga hare-haren da ƴan bindigan ke yawan kai wa garuruwan, suna kuma sace mutane don neman kudin fansa tare da kwasar dabbobi da sauran dukiyoyi.
Wata majiya ta shaida wa BBC, cewa yanzu haka akwai mutum fiye da 20 da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su, tare da neman biya kudin fansa.
Bayanan da BBC ta tattara sun ce ƴan bindigan suna hana jama’ar garuruwan da abin ya shafa sakat, har abin ya kai ga hana jama’a zuwa aiki a gonaki. wani mutumin yankin, wanda ya gwammace a sakaya sunansa, ya bayyana irin halin da suke ciki:
‘‘Da dare ba ka bacci, da rana ba ka zuwa gona, rayuwa na cikin matsala. Halin da muke ciki ma sun yanka mana haraji, na miliyn 10, sai mun haɗa ta…duk mai mata abin da zai bada 21, 500.’’
Mutumin ya ce kusan kullum sai ƴan bindigar sun yi wani nau’in cin mutumci ga jama’a, ko dai a gonaki ko a gida.
Da BBC ta tuntubi Dokta Nasiru Mua’azu, kwamishinan tsaro na jihar ta Katsina, ya yi bayani cewa akwai wani lokaci da ƴan bindigar suka fafata da sojoji kuma har ta kai ga sojojin sun fatattake su tare da ƙwace masu babura, don haka ‘‘ina zargin ramuwar gayya ce ƴanbindigar ke yi a kan jama’a.
Ƴan Bindiga: Ƙofarmu A Buɗe Take Ga Duk Wanda Yake So Ya Miƙa Wuya- Tinubu.
Sojojin Nijar Sun Kashe Ƴan Bindiga 60
Kwanakin Bello Turji Sun Kusa Ƙare Wa- Sojin Najeriya.
Dokta Mu’azu ya ce gwamnati na yin bakin ƙoƙarin ta domin magance wannan matsala, amma a mastayin wani mataki na wucin gadi, in da ‘’jami’an tsaro ke yi wa manoma rakiya har zuwa gonaki da kuma tashin su, na tsawon wata guda.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.