February 23, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Dokin rundunar Sojin Najeriya mai muƙamin Sajan ya mutu a Kaduna.

A jiya Asabar ne runduna ta daya ta sojojin Najeriya, reshen Kaduna, ta gudanar da bikin dokin ta na aiki mai suna Dalet Akawala mai muƙamin Sajan, wanda ya mutu a ranar 24 ga Janairu, 2025.

Jaridar Punch ta rawaito cewa bikin binniyar ya gudana ne a hedikwatar rundunar da ke garin Kawo a Kaduna, inda mataimakin shugaban ma’aikata, Kanar I.A Akabike ya jagoranta.

Akabike ya wakilci babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya da kuma kwamandan sashe na 1 na ‘Operation Fansan Yamma’, Manjo Janar Mayirenso Saraso.

A jawabinsa, Akabike ya jinjina wa marigayi dokin, inda ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin bangare na al’adu tarihin rundunar a wannan yanki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *