Daga Fatima Suleiman Shu’aibu Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Mohammad Abubakar II ya musanta maganar da ake yi cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnoni. Sarkin musulmin ya ce sarakunan gargajiya sun kasance jagorori a ƙasar tun kafin ta samu ƴancin kai, sannan ya ƙara da cewa sarakunan sun fi gwamnonin fahimtar yanayin ƙasar. BBC Hausa […]
An Yi Kira Ga Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Ta’amali Da Miyagun Kwayoyi.
Daga Abdul’aziz Abdullahi An bukaci Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu,ya ayyana dokar ta ɓaci baci kan ta’amali da kwayoyi a ƙasar baki ɗaya. Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabuƙata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation GCAF Amb Auwalu Muhammad Danlarabawa, ne ya yi kiran cikin wata takardar manema labarai da ya sanya wa hannu. […]
Ƴansanda Sun Kama Wani Ɗan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara.
Daga Sani Ibrahim Maitaya Rundunar Ƴansandan jihar Zamfara ta kama wani dan kasar Aljeriya mai shekaru 58 da ake zargi da safarar makamai, in da aka kwato bindigu kirar AK47 guda 16, da wasu ƙanana biyu a hannun sa. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Dalijan ya bayyana haka, a lokacin da ya ke gabatar da […]
Gwamnan Jigawa ya janye dakatarwar da ya yi wa kwamishinansa kan zargin lalata.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi, ya janye dakatarwar da ya yi wa kwamishinansa ayyuka na jihar Auwal Ɗanladi Sankara, bayan da wata kotu a jihar Kano ta wanke shi daga zargin aikata lalata. Janye dakatarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Jigawa Bala […]
Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaddamar Sabuwar Tashar Mota Ta Zamani.
Daga Sani Ibrahim Maitaya Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, ya ƙaddamar da aikin ginin tashar mota ta zamani a Gusau babban birnin jihar. Gwamnan ya ce sabuwar tashar za ta samar da dimbin ayukkan yi ga al’umma. A ranar Litinin aka ƙaddamar da aikin gina tashar ta zamani, a kan titin Sokoto zuwa Zaria a […]
Ƙungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jihar Zamfara.
Daga Sani Ibrahim Maitaya. A Najeriya ƙungiyar kwadago ta ƙasar reshen jihar Zamfara, ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar 1 ga watan Disamba, idan gwamnatin jihar ba ta soma biyan mafi karancin albashi na dubu 70 ba, a ƙarshen wannan wata. Wannan na zuwa ne jim kaɗan da kammala […]
Shugaba Tinubu Ya Isa Brazil Taron G20.
Daga Fatima Suleiman Shu’aibu Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, domin halartar taron shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar G20. A jiya shugaba Tinubu ya bar Najeriya Dan halartar taron kungiyar G20. Obasanjo Ya Nemi A Sauke Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Mahmoodd Yakubu. Kwankwaso Ya Yi […]
Obasanjo Ya Nemi A Sauke Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Mahmoodd Yakubu.
Daga Fatima Suleiman Shu’aibu Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi kira da a yi garambawul na gaba ɗaya ga tsarin zaɓen ƙasar. Da yake jawabi a taron Chinua Achebe Leadership Forum, Jami’ar Yale, a Amurka, Obasanjo ya yi kira musamman da a tsige Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), […]
Kwankwaso Ya Yi Zargin Ana Neman Yi Musu Dole Daga Lagos A Harkar Masarautun Kano.
Daga Fatima Suleiman Shu’aibu Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (NNPP) a zaɓen 2023 kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi shirin da jihar Legas ke yi na yin mulkin mallaka a yankin Arewa. Kwankwaso, ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron yaye ɗalibai […]
Matashi Ya Kashe Kansa Sanadin Sauraron Kiɗan Gangi A Kano.
Daga Fatima Suleiman Shu’aibu Rundunar Ƴansandan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Garba, da ke garin Butu Butu a ƙaramar hukumar Rimin Gado ta jihar, sanadin sauraron kiɗan gangi da ya kunna ƙila don nishaɗi. Kakakin rundunar Ƴansandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce “matashin […]
Tsadar Rayuwa: Ba Da Daɗewa Ba Abubuwa Za Su Yi Kyau -Gwamnatin Najeriya.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin, ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar matsaloli, amma ya ba da tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba lamarin zai sauya da kyau. Yayin da Tinubu ya nanata cewa gwamnatinsa na kan hanya, ya kuma lura cewa mafita ga al’amuran da ke faruwa […]
Trump Na Gaba-Gaba A Sakamakon Zaɓen Amurka.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Trump na kan gaba a sakamakon farko-farko da ya fara fito wa a zaɓen Amurka, in da ya yi wa abokiyar karawarsa Kamala fintinkau. Zuwa yanzu Donald Trump na da kuri’un wakilan zaɓe 230 ya yin da Kamala Haris ta ke da 185, bayan Trump ya samu ƙuri’u 58,915,044 yayin da […]
Gwamnatin Kano Za Ta Fara Tantance Baƙi Ƴan Kasashen Waje Da Ke Jihar.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin ƙwararru da zai yi aikin yi wa baƙi ƴan ƙasashen waje mazauna birnin rijista musamman waɗanda suke gudanar da kasuwanci. BBC ta rawaito gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin samun alƙaluman mutanen da suka fito daga ƙasashen ƙetare kuma suke gudanar da […]
Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo A yan kwanakin nan rikicin cikin gida a jam`iyyar NNPP a jihar Kano na ƙara ɗaukar sabon salo tun bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar, ta yi zaɓen ƙananan hukumomi, daman kafin nan batun fitar ƴan takarara ne ya fara bayyana irin tarin rikicin da jam’iyyar ke fama […]
Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Da Kwalejojin Najeriya Sun Janye Yajin Aiki
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Kungiyar ma’aikatan jami’o’i da kwalejoji da ba na bangaren koyarwa ba, NASU da SSANU sun janye yajin aiki na tsawon wata guda, daga ranar 5 ga watan Nuwamba janyewar za ta fara aiki. Daily Nigerian ta rawaito, babban sakataren kungiyar, Peters Adeyemi me ya baiyana hakan a wata samarwa da ya […]
Gwamnan Gombe Ya Sa Hannu Kan Takardar Yarjejeniyar Samar Da Tashar Wutar Lantarki A Jihar.
Daga Abdul’aziz Abdullahi Gwamnatin jihar Gombe ta kulla yarjejeniyar da wani shararren kamfani mai suna China18th Engineering, wanda zai samarwa jihar tashar wutar lantarki megawatt 100 mai amfani da hasken rana (Solar). Gwamna Inuwa Yahaya, ya rattaba hannun kan takardar yarjejeniyar a gidan gwamnati da ke Gombe, in da ya bayyana muhimmancin samar da tashar […]
Akwai Bindigogin AK47 Guda Dubu 60 A Sansanonin Ƴan Bindiga Ɗari 120 Cikin Jihohin Arewa Masu Yamma,-Rahoto.
Daga Sani Ibrahim Maitaya. Wani Farfesa a jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto a Najeriya Farfesa A. G Yahayya ya ce, rashin tsaro ya sa matsa sama da miliyan ashirin yan tsakanin shekaru 20 zuwa 40, ba su da aikin yi a jahohi shidda na Arewa Maso Yammacin Najeriya. Farfesa A. G Yahayya ya bayyana […]
Gwamnan Bauchi Ya Buƙaci Gwamnatin Najeriya Ta Saki Yaran Arewa Da Take Tsare Da Su A Abuja.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo A wani saƙo da ya wallafa a shafin na Facebook mai taken #ArewaMuFarka gwamnan jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya Sanata Bala Muhammad Abdulƙadir, ya buƙaci ƴan Arewacin ƙasar da su tashi su farka musamman malamai, iyaye da shugabanni. A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu hotunan da bidiyon da […]
Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Biyan Dubu 72 Mafi Ƙarancin Albashi A Kaduna.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya amince da naira 72,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ga ma’aikatan jihar. BBC ta rawaito, cikin sanarwa da sakataren watsa labarai na jihar, Ibraheem Musa ya fitar, ya ce ƙarin zai fara aiki daga watan Nuwamban da ke […]
Babu Wata Barazana Game Da Ƙarancin Mai A Najeriya,-Manyan Dillalan Man Fetur.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Manyan dillalan man fetur a Najeriya, sun tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa akwai wadattacen man fetur a ƙasar, don haka ‘yan ƙasar su kwantar da hankalinsu. BBC ta rawaito, Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar manyan dillalan, Clement Isong, ya fitar ranar Laraba ya ce akwai wadattacen mai a rumbunan ajiyar […]
APC Ta Gargaɗi Gwamnan Kano Kan Gudanar Da Zaɓe Ƙananan Hukumomi Gobe Asabar.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Shugaban jam’iyyar APC mai adawa a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya gargaɗi gwamna Abba Kabir Yusuf, da ka da ya kuskura ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi “kamar yadda wata kotu bayar da umarni.” BBC ta rawaito, a wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ranar Juma’a a Abuja, Abdullahi Abbas […]
Ƴan bindiga Sun Sanya Harajin Miliyan 10 Ga Wasu Ƙauyuka A Jihar Katsina.
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, al’ummomin wasu garuruwa shida na yankin ƙaramar hukumar Danmusa, sun ce suna cikin halin ƙaƙa-nika-yi, sakamakon harajin naira miliyan goma da ƴan bindiga suka ƙaƙaba masu, baya ga hare-haren da ƴan bindigan ke yawan kai wa garuruwan, suna kuma sace mutane don neman kudin fansa tare da kwasar dabbobi […]
Wani Babban Kwamandan Sojin Isra’ila Ya Baƙunci Lahira A Gaza.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Sojojin Isra’ila sun ce an kashe wani kwamandan da ke tuka wata tankar yaki a arewacin Gaza. Rahotanni sun bayyana cewa tankar da Kanal Ehsan Daqsa ke ciki ce ta daki wani abin fashewa lokacin da suke kai hare-hare a Jabaliya. Hezbollah Ta Fatattaki Sojojin Isra’ila A Ƙoƙarinsu Na Kutsawa Lebanon. […]
An Sake Kama Wani Mutum Da Bindigogi A Yayin Da Trump Ke Yaƙin Neman Zaɓe.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Jami’an tsaron Ƴansanda a jihar California ta Amurka sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi a cikin motarsa kusa da wani guri da ɗan takarar shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ke yin gangamin yaƙin neman zaɓe. BBC ta ce, an bayar da belin mutumin wanda aka tsare a wani shingen binciken […]
Mutum Sama Da 20 Sun Mutu A Wani Harin Da Sojoji Su Ka Kai Kasuwa A Sudan.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo. Wasu rahotanni na cewa harin rundunar sojin Sudan ya kashe mutane aƙalla 23 da kuma raunata wasu fiye da 40 a kudancin birnin Khartoum. BBC ta rawaito, an kai harin ne a kan babban sansanin mayaƙan RSF a kudancin Khartoum, amma ya kuskure, in da ya faɗa a kan wata babbar […]
An Ba Wa Ganduje Wa’adin Kwanaki 7 Ya Sauka Daga Shugabancin Jam’iyyar APC.
Daga Sani Ibrahim Maitaya Wani jigo a jam’iyyar APC Alhaji Saleh Zazzaga, ya sabunta yunkurin tsige shugaban jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, ta hanyar neman ya sauka daga mulki cikin kwanakki bakwai. Sabon yunƙurin na Zazzaga na zuwa ne a dai-dai lokacin da ya kasa samun nasara a yunƙurin sa na tsige Ganduje, ta […]
Za Mu Yi Ƙoƙarin Rage Kuɗin Aikin Hajjin Bana – NAHCON.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Yayin da maniyata aikin hajjin bana a Najeriya ke cikin rashin tabbas kan tsadar kujerar zuwa ƙasa mai tsarki don sauke farali, shugaban hukumar jin daɗin alhazai NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ce hukumar tana ƙoƙari domin tabbatar da kuɗin Hajjin bai kai yadda ake hasashe ba, in da ya […]
Hezbollah Ta Fatattaki Sojojin Isra’ila A Ƙoƙarinsu Na Kutsawa Lebanon.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wasu rahotanni na cewa, Hezbollah ta ce ta yi ma sojojin Isra’ila kwanton ɓauna da daddare da abubuwa masu fashewa yayin da suke ƙo ƙarin kutsawa cikin Lebanon a kan iyakar ƙasar da Isra’ila da ke gabashin Lebanon. BBC ta rawaito, ƙungiyar ta kuma ce ta yi nasanar korar wasu sojojin […]
Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Najeriya Ta Yi Ƙarin Girma Ga Wasu Jami’anta A Jihar Gombe.
Daga Abdul’aziz Abdullahi A Najeriya hukumar kula da shige da fice ta ƙasar wato Nigeria Immigration Service (NIS) reshen jahar Gombe, ta yi ƙarin girma ga wasu jami’an ta domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa akan ayyukan su. Da ya ke jawabi a ya yin wani biki da ya gudana a dakin taro na sakatariyar gwamnatin […]
Ƙungiyar Hezbollah Ta Harba Rokoki Kan Runbun Jiyar Makaman Isra’ila A Tsakar Daren Jiya.
Rahotanni na cewa, kungiyar Hezbollah ta ce ta kai harin a kan rumbun makaman Isra’ila da ke Dishon da Dalton duka a arewacin Isra’ila da manyan rokoki. Ta ce, ta harba wasu rokokin zuwa a kan “matattarar maƙiya” da ke Yir’on, wanda wani yanki ne a arewacin ƙasar da ke kusa da kan iyakar Lebanon. […]
Ƴan Bindiga Sun Halaka Askarawa 8 A Jihar Zamfara.
Daga Sani Ibrahim Maitaya Wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe jami’an ba da kariya ga al’ummar jahar Zamfara da aka fi sani da ASKARAWA su takwas, a wani harin kwantan ɓauna da suka kai a karamar hukumar mulkin Tsafe ranar Litinin. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidabwa mjiyar mu […]
Babban Sifeton Ƴansanda Ya Umarci Jami’ansa Su Janye Daga Sakatariyar Ƙananan Hukumomin Jihar Rivers.
Wasu rahotanni daga jihar Rivers na cewa, babban Sufeto na ƴansandan Najeriya ya ba da umarnin janye jami’ansu da su ka mamaye sakatariyar ƙananan hukumomi a Rivers na tsawon watanni uku. An mamaye sakatariyar ne a watan Yuni sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakanin shugabannin kwamitin riko da ke goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara […]
Fadar Shugaban Najeriya Ta Karrama Shugaban Makarantar Sakandare A Jihar Zamfara.
Daga Sani Ibrahim Maitaya An karrama wani shugaban makarantar sakandare daga jahar Zamfara a matsayin wanda ya fi kowa kwazo a faɗin ƙasar nan da lambar yabo ta fadar shugaban ƙasa ta malamai daga makarantun najeriya a 2024. Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume shine ya sanar tare da bayar da kyautukka ga malaman da […]
Kuskuren Jaridar Daily Trust Da Yadda Gaskiya Ta Bayyana Game Da Yarjejeniyar Samoa.
Daga Abdulaziz Abdulaziz A ranar Laraba da ta gabata jaridar Daily Trust ta fito da jawabin neman afuwa ga gwamnatin tarayya game da labarin da ta wallafa marar tushe kan zargin cewa akwai goyon bayan auren jinsi a cikin yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta Samoa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanyawa hannu. Neman afuwar […]
Gwamnan Jihar Zamfara Ya Biya Naira Biliyan 9 Ga Ƴan Fansho.
Daga Sani Ibrahim Maitaya Gwamnan jahar Zamfara da ke Arewacin Najeriya, Dauda Lawal, ya biya N9,357,743,281.35 a matsayin kuɗaɗen gratuti da ma’aikatan da su ka yi ritaya a jahar Zamfara ke bi bashi tun daga 2011. Gwamnan ya amince da fara biyan kuɗaɗen ne a watan Fabrairun bana. A cikin wata sanarwa da mai magana […]
Ƴan Bindiga: Ƙofarmu A Buɗe Take Ga Duk Wanda Yake So Ya Miƙa Wuya- Tinubu.
Daga Suleman Ibrahim Moddibo. Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce za a cigaba da luguden wuta a kan ƴanbindiga da ɓarayin daji da masu satar man fetur da sauran ɓata-garin da suke addabar Najeriya matuƙar ba su daina ta’addancin da suke yi ba. BBC Hausa ta rawaito, Tinubu ya bayyana hakane a ranar Alhamis a […]
Gwamnatin Jihar Adamawa Za Ta Tantance Ma’aikata.
Daga Nuruddeen Usman Ganye Gwamnan Kano jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayar da umarnin cewa duk ma’aikatan da ke aiki a ma’aikatun gwamnati da su gaggauta gabatar da takardun karatun su, domin tantance su. Gwamnan ya bada umarnin ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ta hannun babban sakataren yada labaran […]
Kwanakin Bello Turji Sun Kusa Ƙare Wa- Sojin Najeriya.
Daga Sani Ibrahim Maitaya Shugaban rundunar tsaro ta kasa Christopher Musa, ya sanar da cewa kwanaki kaɗan ne suka ragewa riƙaƙƙen ɗan ta’adda Bello Turji a duniya. A cewar Christopher Musa aikin yaƙi da ta’addanci da rundunar soji ke yi a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan, ya jefa fargaba da tsoro ga sansanin Bello […]
Za Mu Ɗauki Matakin Da Ya Dace Kan Isra’ila Ta Ƙarfin Tuwo.-Khamene.
Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yaba da hare-haren da Iran ta ƙaddamar kan Isra’ila ranar Talata, inda ya kira su da cewa hare-hare da ke kan ‘ƙa’ida”. Yayin da yake gabatar da huɗumar Juma’a a birnin Tehran, Mista Khamenei ya ce abin da suka yi ”ɗan ƙaramin hukunci” ne kan Isra’ila saboda ”laifukan […]
Najeriya Ta Fi Samun Tsaro A Mulkin Tinubu -Nuhu Ribadu.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Mai bai wa shugaban ƙasar Najeriya shawara kan sha’anin tsaro Mallam Nuhu Ribadu, ya bigi ƙirji cewa ƙasar ta fi samun ingantuwar tsaro a mulkin shugaba Tinubu idan aka kwatanta da zamanin gwamnatin da ta gabace su. TRT ta rawaito, Ribadu na cewa “Ina tabbatar muku cewa a yau Abuja ta […]
Sojojin Nijar Sun Kashe Ƴan Bindiga 60
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wasu rahotanni daga jamhuriyar Nijar na rundunar sojin ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga sama da 60 da kuma ƙwato shanu 250 da ‘yan bindigar suka sace. BBC ta rawaito cewa, sojojin sun samu wannan nasara ne a wani aiki da suka aiwatar na haɗin-gwiwa a jihar Tillabery da kuma […]
Gwamnatin Kano ta ciyo bashin biliyan 177.4 daga ƙasar Faransa.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo A shirin ta na samar da ruwan sha, gwamnatin jihar Kano ta Abba Kabir Yusuf, ta ciyo bashin Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Cigaban Faransa wato French Development Agency domin samar da ruwan sha a jihar. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Ruwa na jihar, Alhaji Ali Haruna Makoɗa ya […]
Sauyin Yanayi: Najeriya ta bayyana barnar da Ambaliyar ruwa ta yi a Borno da Zamfara a taron majalisar kasashen Afrika.
Nijeriya ta bukaci masu hannu da shuni a fadin duniya da su tallafawa kasashen Afrika da sauyin yanayi ya shafa. Mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa, Benjamin Okezie Kalu kuma shugaban tawagar Nijeriya a ci gaba da zaman majalisar wakilai daga kasashen Afrika dake gudana a kasar Afrika ta Kudu a ranar Talata inda ya […]
Tsohon Shugaban Amurka Trump Ya Tsunduma Harkar Crypto.
Tsohon shugaban kasar Amurka, Donal Trump tare da ‘ya’yan sa sun kaddamar da manhajar hada-hadar kudi ta yanar gizo da aka fi sani da cryptocurrency. Ba a yi wani cikakken bayani ba kan tsarin crypto din da Trump, wanda shi ne dan takara shugaban kasa a jam’iyyar Republican da ahalinsa su ka samar a wani […]
Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Birnin Maiduguri.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wasu rahotanni da ke fitowa daga jihar Borno na cewa, al’umma mazaunin birnin Maiduguri sun shafe daren jiya ba tare da bacci ba, saboda mummunar bala’in Ambaliyar Ruwa da ta mamaye birnin. Jama’a da dama ne suka taru a kofar fadar Shehun Borno, in da suke neman mafaka, ko da dai […]
Rashin adalci ne a bada rabon tallafin shinkafar Kano a hannun APC – Kwankwaso.
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin gamsuwa kan yadda gwamnatin tarayya ta bada aikin rabon tallafin shinkafa da kuma batun tafiyar da tsaro a jihar Kano. A wani sako da ya wallafa a shafin X, Kwankwaso ya bayyana damuwa kan yadda aka bai wa Gwamnonin jihohi 35 shinkafar don rabawa […]
DSS Sun Cafke Shugaban NLC Joe Ajaero.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wasu rahotanni a Najeriya na cewa jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama shugaban kungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) Joe Ajaero. Yansanda Sun Tsare Mutumin Da Ya Caka Wa Ƴar shekara 8 Almakashi Da Cokali A Al’aurarta Har Sai Da Ta Sume. Biyan kudin fansa ba ya hana ƴan […]
Yansanda Sun Tsare Mutumin Da Ya Caka Wa Ƴar shekara 8 Almakashi Da Cokali A Al’aurarta Har Sai Da Ta Sume.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar Ƴansandan jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, ta tsare wani mutum mai shekara 32 bisa zargin caka wa wata yarinya mai shekara 8 almakashi a gabanta. Mutumin ya yi wa yarinyar mummunan rauni a gabanta har sai da ta sume, a sakamakon wannan aika-aika da ya yi mata. Aminiya ta […]
“Ku tabbatar cewa ba a sake kawo taliya mutane sun karɓa ba”-Kwankwaso.
Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyar PDP mai hamayya a ƙasar ta mutu a fagen siyasar ƙasar. Yayin da yake jawabi a ofishin jam’iyyar NNPP na jihar Katsina ranar Asabar, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam’iyyar APC ta jefa kanta cikin abin da ya kira ”halaka”. ”Jam’iyyar PDP dama kowa […]
Gagarumar Zanga-zanga Ta `Barke A Isra’ila Yayin Hezbollah Ke Zafafa Hare-hare Kan `Kasar.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wasa rahitanni daga `kasar Isra’ila na cewa, gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a biranen Isra’ila, don neman gwamnatin ta dawo da ‘yan ƙasar da Hamas ke garkuwa da su a Gaza. BBC ta rawaito masu shirya zanga-zangar sun ce kusan mutum 500,000 ne suka fantsama kan tittuna a Tel Aviv, tare da […]
Musulman Najeriya Sun Daga Tutar Mauludin Annabi S A W.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wasu al’ummar Musulmai mabiya ɗariƙar Qadiriyya a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, sun daga tutar Mauludin Annabi Muhammad S A W, a hedkwatar ɗariƙar ta Afirka da ke birnin Kano. Shugaban ɗariƙar Qadiriyya ta Afirka, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, ne ya jagoranci ɗaga tutar tare da ɗaruruwan mabiyansa. Daman sun […]
Ƙungiyar Limamai A Najeriya Na Son Gwamnati Ta Gyara Matatun Mai Na Ƙasar.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wata ƙungiyar limaman Juma’a mabiya ɗariƙar Qadiriyya a Najeriya sun Buƙaci kamfanin samar da Man Fetur na ƙasar NNPCL ya sassauta farashin Mai cikin gaggawa, don sama wa al’ummar ƙasar da ke shan wahala sauki, sanadin ƙarin kuɗin Mai. Kungiyar ta ce kiran nasu ya zama wajibi domin nema wa al’umma […]
Zancen Man Fetur Ya Sauka Zai Yi Wahala, -Ɗangote.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo da Fatima Suleman Suleiman Shu’aibu Shugaban rukunin kamfanonin Dangote kuma mamallakin matatar Man Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa babu yuwuwar samun saukin farashin mai a najeriya a yanzu duk kuwa da cewa matatar man sa zata fara siyar da Mai nan ba da jimawa ba Dangote ya bayyana hakan […]
Gini Ya Danne Mutum 2 Sun Mutu A Jihar Kano.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rahotanni a jihar Kano na cewa, an tabbatar da mutuwar mutum biyu, wasu biyu kuma sun tsallake rijiya da baya, a sakamakon rushewar wani bene mai hawa biyu a Jihar Kano. Aminiya ta rawaito cewa, da misalin ƙarfe biyu a dare kafin wayewar garin ranar Alhamis ne benen ya rushe da […]
SSANU Ta Sake Yin Kira Ga Gwamnatin Najeriya Kan Biyan Albashin Watanni 4 Da Aka Hana Su.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU, ta sake jaddada kiran a gaggauta biyan albashin mambobinta na watanni hudu da aka hana su albashi. Shugaban ƙungiyar SSANU Mohammed Ibrahim, ne ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, a ƙarshen taron majalisar zartarwa na kasa. […]
Ba ƙwace motocin sojoji ƴan bindiga su ka yi ba – Mazauna Zamfara.
Wasu mazauna garin Zurmi da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara sun karyata rade-radin da ake ta yadawa na kwace wasu motoci biyu dauke da makamai daga hannun sojoji da wani dan bindiga mai suna Bello Turji ya yi. Da ya ke zantawa da Daily Trust, wani mazaunin garin Zurmi ya ce ‘yan bindigar […]
Crypto: Kotu ta Aike Wa Gwamnan CBN Sammmaci Don Ya Gurfana A Gaban Ta.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta aika sammaci ga Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, Olayemi Cardoso da ya bayyana a gabanta game da shari’ar da ake yi wa kamfanin crypto na Binance. The Cable ta rawaito cewa kotun ta ce Cardoso zai bayyana gaban ta da wasu takardun […]
Kotu: An Tsare Ɗan Jarida A Gidan Yari Kan Zargin Ɓata Sunan Gwamnan Kano Abba.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wata Kotu a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, ta ba da umarnin a tsare mata wani Ɗan Jarida da aka gurfanar a gabanta kan zargin ɓatancin ga gwamna Abba Kabir Yusuf. Tin da farko Ƴansanda ne suka fara tsare matashin Ɗan Jaridar mai suna Muktar Dahiru kafin daga bisani su […]
Gwamnatin Najeriya Ta Bai Wa Ƴan Kasuwa Wa’adin Tata Ɗaya Su Rage Farashi.
Hukumar kula da hakkin mai siye ta tarayya FCCPC, ta bai wa ‘yan kasuwa wa’adin wata guda da su rage farashin kayayyakin da suke siyarwa. Sabon shugaban hukumar, Mista Tunji Bello ne ya sanar da hakan a yayin taro da masu ruwa da tsaki don magance tsawwala farashin kayayyki da ya gudana a ranar Alhamis […]
Amnesty Ta Nemi A Saki Ɗan PDPin Da Ke Tsare A Sokoto Kan Wallafa Bidiyon Gwamna Da Matarsa.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin jihar Sokoto da hannu wajen kame wani matashi ɗan jam’iyyar PDP mai amfani da shafukan sada zumunta, Shafi’u Umar Tureta. Daily Trust ta rawaito, a cikin wata sanarwa da ta fitar, Amnesty ta ce Ƴansandan suke dauke da muggan makamai suka […]
Cutar Kyandar Biri Ta Yaɗu Zuwa Jihohin Najeriya 19.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Zuwa yanzu cutar Kyandar Biri na ƙara ɓarkewa a Najeriya in da ta yaɗu zuwa wasu jihohi 19 na ƙasar da kuma babban birnin tarayya Abuja in da ta kama mutum 40. Daily Trust ta rawaito, a wani rahoto daga cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ya kuma nuna cewa […]
Aikin Da Aka Yi Na Gyaran Bakarantu Ba Gwamnatin Kano Ce Ta Yi Ba, Kuɗin AGILE Ne Na World Bank-Ƙiru.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kano a lokacin tsohuwar gwamnatin Ganduje, Muhammad Sunusi kiru, ya ce ba gwammatin Jihar Kano ce ke gyaran makarantu da ake gani ba a jihar, Shirin AGILE ke yi. Da yake tsokaci a shafin sa na Facebook, Ƙiru ya yi zargin ana yi wa shirin AGILE […]
An Shekara Sama Da 5 Ba A Ɗauki Malami Ko Ɗaya Ba A Jihohin Najeriya 18 Ba-NUT.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Kungiyar Malmai ta Najeriya NUT ta ce zuwa yanzu akwai jihohin Najeriya 18 waɗanda suka kwashe sama da shekaru biyar ba a ɗauki malamin makaranta ko guda ɗaya ba. RFI rawaito cewa, hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da aka gaza samun daidaito kan ƙarancin malamai a fadin kasar, […]
Gwamnatin Neja Ta Janye Dakatar Da Haƙar Ma’adinai A Jihar.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, ta dage dakatarwar da ta yi wa duk wasu masu ayyukan hakar ma’adinai a faɗin jihar. Mukaddashin gwamnan jihar, Yakubu Garba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin yaƙi da hako ma’adinai da lalata muhalli ba bisa ƙa’ida ba […]
Rasha Na Ɗada Zafafa Hare-haren Makamai Masu Linzami Da Jirage Marasa Matuƙa A Birnin Kyiv Na Ukraine.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Wasu Rahotanni daga Kyiv na cewa an ji ƙarar fashewar bama-bamai aƙalla sau 33 da tsakar dare. Sojin da ke kula da birnin sun sanar da lalata makamai masu linzami ta amfani da na’urar kare sararin samaniya. BBC ta ce, mai sharhin labarin wasanni a gidan talbijin ɗin ƙasar Vitali Volochai, […]
Ɗan Wasan Gaban Najeriya Da Napoli Osimhen Ya Nemi Chelsea Ta Rika Biyansa Fam £500, 000 Duk Mako.
Daga Suleman Ibrahim Tauraron dan wasan ƙwallon ƙafa a Afirka, wanda ke taka leda a ƙungiyar Napoli Victor Osimhen ya buƙaci Chelsea ta rika biyansa albashin fam £500, 000 duk mako kafin ya amince da komawa kungiyar a cewar jaridar The Sun, Idan har Osimhen ya aminta da da yarjejeniyar ƙungiyar Chelsea zai iya fara […]
Ambaliya: Mutum Kusan 50 Sun Rasu In Da Dubbai Suka Rasa Muhallansu A Najeriya.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Aƙalla mutum 49 ne suka mutu, sannan dubbai suka rabu da muhallansu bayan mamakon ruwan sama da ya jawo ambaliya a Arewacin Najeriya, kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya ta sanar a ranar Litini. BBC ta rawaito, a jihohin Arewa guda uku da suka fi fuskantar ambaliyar su […]
An Kammala Yarjejeniya Da Sabon Kocin Super Eagles Ta Najeriya.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta kammala yarjejeniya da Bruno Labbadia a matsayin kocin Super Eagles. Babban sakataren NFF, Dr. Mohammed Sanusi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Safiyar a Yau Talata. “Kwamitin zartarwa na NFF ya amince da shawarar naɗa Bruno Labbadia a matsayin […]
Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga A Dazukan Kaduna Da Zamfara.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo A wasu hare-hare da rundunar sojin saman Najeriya suka kaddamar sun kashe tarin ƴan ta’addda a Kaduna da Zamfara. RFI ta rawaito, Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin saman, Edward Gabkwet ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi a Abuja. Mr Gabkwet ya ce rundunar […]
Allah ya yi wa Sarkin Ningi Alhaji Yanusa Ɗanyaya rasuwa.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rahotanni a jihar Bauchi da ke Najeriya na cewa, Allah ya yi wa mai martaba sarkin masarautar Ningi da ke jihar rasuwa Alhaji Yanusa Muhammad ɗanyayaa ranar Lahadi. Da ya ke tabbatar da rasuwar cikin wani saƙo da aka yaɗa ta kafofin sada zumunta, sakataren fadar Ningi Alhaji Usman Sule Maga […]
Iyalan Sarkin Kano Ado Sun Ƙaryata Alaƙa Da Zainab Wadda Take Iƙrarin Ita Ɗiyar Sarkin ce.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo. Iyalan marigayi mai martaba Sarkin Alhaji Ado Bayero, sun nesanta kansu daga duk wata dangata da wata mata da ake cewa matar marigayi Sarki Kano na 13 ce a jihar Edo. Cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun Aminu D.Ahmad, tsohon babban jami’in tsaron […]
Ba Mu Bayar Da Umarnin Al’umma Su Ɗauki Makamai Don Kare Kansu Daga Ƴan Bindiga Ba- Gwamnatin Katsina.
Daga Abdulrahman Salihu Gwamnatin jihar katsina, ƙarƙashin jagoranci Malam Dikko Umar Radda, ta yi ƙarin haske kan bayanan da ke yawo bisa matakan da take dauka kan sha’anin tsaro. A ranar Alhamis ne wasu rahotanni suka fara yawo a kafafen sada zumunta, in da ake yaɗa cewa, gwamnatin jihar ta yi umarni al’ummar jihar su […]