Labarai

Labarai

Matashi Ya Yiwa Mahaifin Budurwarsa Mummunan Rauni Bayan Ya Hana Shi Kaiwa Dare Idan Yaje Zance.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Saurayin ya yiwa mahaifin budurwarsa rauni ne bayan da baban budurwar tasa ya hana shi kaiwa dare idan yaje zance a garin Ɗan Hassan, da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Arewa Radio ta rawaito cewa, an jiwa mahaifin budurwar raunine bayan da ya umarce saurayin […]

Read More
Labarai

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata. Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau. Haka nan sun […]

Read More
Labarai

Lauyan Gwamnatin Kano Ya Nemi Kotu Ta Yiwa Abduljabbar Hukunci.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci. Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari’ar sun gabatar da Jawabansu na karshe […]

Read More
Labarai

Jami’an Tsaro Sun Gano Jaririn Da Aka Sace Kusan Mako Guda A Wani Asibitin Jihar Bauchi.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Hukumar asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, da ke jihar Bauchi a Arewacin Najeriya, ta ce an gano jaririn da aka sace a asibitin a makon jiya. Dr. Haruna Liman mataimakin shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewan, yace an samu jaririn ne cikin daren ranar Litinin da misalin […]

Read More
Labarai

Atiku Ya Taya Musulmi Murnar Mauludin Annabi SAW Wanda Ya Siffanta Shi Da Mai Jin Ƙai.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Ɗan takarar shugaban Ƙasar Najeriya a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya taya al’ummar musulmi a Najeriya murnar zagayowar watan da aka haifi Annabi Muhammad S A W. Atiku ya taya murnar ne a shafin sa na Facebook a ranar Talata. “Jinkai, adalci, tausayi, son Zaman lafiya da Haɗin kai da Amana […]

Read More
Labarai

Wannan Shine Karo Na 7 Da Wutar Lantarki Ke Ɗaukewa Baki Ɗaya A Najeriya Cikin Shekarar 2022.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Kwanaki masu amfani da wutar lantarkin a Najeriya na murnar wadatar da aka samu, ana cikin haka wutar lantarkin ta dauke baki ɗaya. Hukumar samar da wutar lantarki ta danganta ci gaban da aka samu na wadatar wutar da sakamakon daidaita wasu kwangiloli da ake ganin suna da alhakin gazawar da […]

Read More
Labarai

Kotu Tsare Matashi Watanni 20 Tare Da Biyan Diyya Dubu  50, Bayan Ta Same Shi Da Laifin Saran Wani.

Daga Fa’izu Muhammad Magaji Wata kotun shari’ar Muslunci mai lamba 2 a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, ta tsare wani matashi watanni 20 a Kurkuku, kutun tayi hukuncin ne bayan samun wanda ake zargin da laifin saran wani da Adda. Kutun ta kuma samu wanda ake zargin mai suna Haidar Abdullahi, Da […]

Read More
Labarai

Ɗan Turkiyya: Yana Iƙrarin Kashe Kansa, Ya Cakawa Kansa Wuƙa Sai Naji Tsoro A  Nima Kada Ya zo Ya Cutar Dani.- Ƴar Kano.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da samun ƙorafi daga wata budurwa da aka sakaya sunanta kan wani saraurayinta ɗan ƙasar Turkiyya da ke bibiyarta bayan sun shafe watanni uku suna tare. “Mun samu ƙorafi daga wannan matashiya kan ta kawo kanta nan shelkwatar yan sanda da ke nan Bomfai tana […]

Read More
Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kama Mushen Dabbobi A Manyanka.

Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki ta Jihar Kano (CPC), ta ce ta kama mushen dabbobi a mayankar ’Yan Awaki da ke Unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni da ke jihar. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Yakasai, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ga manema labarai […]

Read More
Labarai

Kotu Ta Aike Da Matashi Gidan Yari Saboda Satar Goyon Masara 22.

Daga Fa’izu Muhammad Magaji Alkalin kotun shari’ar Muslunci mai lamba 2 da ke zaune a Tashar Babiye a jihar Bauchi Barrister Muktar Adamu Bello Dambam, ya yanke wa wani matashi mai suna Attahiru Dahiru, ɗan shekara 20, mazaunin unguwar a New GRA a garin Bauchi, hukumcin ɗaurin watanni 8 a gidan gyaran hali da tarbiya, […]

Read More