Daga Fatima Suleiman Shu`aibu
Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa a Najeriya EFCC ta cafke Misis.
Joy Enwa, Akanta Janar na jihar Delta, a wani bangare na bincike kan zargin karkatar da naira tiriliyan 1.3 da ake alakantawa da tsohon Gwamna Ifeanyi Okowa.
kazalika Hukumar ta kuma yiwa wasu
jami’ai tambayoyi da suka hada da tsohon Daraktan kudi da kuma wani babban jami’in fadar gwamnatin jihar ta Delta.
A cewar majiyoyin EFCC, kudaden da ake zargin sun hada wani bangaren da rabon rarar man fetur da ake warewa
jihohi da ake hako mai na kashi 13 cikin 100.
A watan Nuwamba, an tsare tsohon Gwamna Okowa a ofishin EFCC na Fatakwal, bisa zargin yin amfani da ofishin sa wajen karkatar da kudaden jihar don biyan bukatun kansa.
Da yake tabbatar da kamen, mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya ce, an tsare uwargida Enwa ne domin
amsa tambayoyi kan binciken da ake yi na karkatar da kudaden jihar a karkashin tsohuwar gwamnatin.
An kuma yi wa wasu jami’an gwamnati tambayoyi.” Misis Enwa, wacce ta kasance mataimakiyar Akanta Janar a lokacin gwamnatin Gwamna Emmanuel Uduaghan, Okowa ya nada ta a matsayin Akanta Janar a shekarar 2020.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP