January 22, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnan Kaduna ya Ƙaddamar da Asibiti da Cibiyar Fasaha, shekara 1 bayan harin bam a ƙauyan Tudun Biri.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Shekara ɗaya bayan da sojoji su ka kai harin bam a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi bisa kuskure,

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙaddamar da cibiyar kula da lafiya a matakin farko mai gadaje 25, haɗi da cibiyar koyar da sana’o’i da , tiyata, da kuma kula da idanu.

Gwamnan ya kuma raba buhu 300 na shinkafa mai nauyin kilogram 50kg, buhunan masara guda 300, da taki buhu 500 ga al’ummar Tudun Biri da ƙauyukan da ke kewaye da garin .

Kafar yada labarai ta Aminiya ta rawaito cewa kimanin mutanen ƙauyen 100 ne aka kashe a watan Disambar 2023, lokacin da wani jirgin soja mara matuƙi na Sojojin Najeriya ke bin sahun ‘yan bindiga, in da su ka sakarwa mutatan garin bama-bamai bisa rashin sani lokacin da suke tsaka da bikin Mauludi a cikin dare .

Bayan haka gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin samar da ababen more rayuwa kamar tituna, ruwan sha, makarantu, asibitoci, da cibiyar koyon sana’o’i ga al’ummar garin.

Gwamnatin Najeriya za ta kammala gyaran matatar mai ta Kaduna zuwa ƙarshen Disamban 2024.

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Biyan Dubu 72 Mafi Ƙarancin Albashi A Kaduna.

Kotun Ɗaukaka Ƙara A Kaduna Ta Sanya Ranar Fara Shari’a Kan Rikicin Sarauta A Masautar Zazzau.

A yayin da yake kaddamar da cibiyar kula da lafiya matakin farko mai gadaje 25 da motar daukar marasa lafiya da kuma cibiyar koyon sana’o’i, haɗi da sashen kula da lafiya, tiyata, da kula da idanu a ranar Lahadi

Gwamna Sani ya yi wa mutanen ƙauyen da su ka rasa ‘yan uwansu alƙawarin cewa zai ci gaba da bin diddigi har sai an kammala bincike, an kuma gurfanar da waɗanda su ka aikata laifin gaban kotu.

A cewar Gwamnan, an shirya gabatar da ayyuka da dama domin cika shekara ɗaya da kuma samarwa da mazauna ƙauyan abubuwan da suke buƙatar.

“Gwamnatinmu ta ba da fifiko wajen bunƙasa al’umma ta hanyar ba su jari kasancewar ita ce hanya mafi inganci na fitar da mutane daga ƙangin talauci”, in ji Gwamnan.

Kazalika Cibiyar Fasaha za ta baiwa matasan Tudun Biri sana’o’in dogaro da kai, wanda zai ba su damar zama ma’aikata, cibiyar Kiwon Lafiya za ta himmatu wajan kula da lafiyar jama’a da kuma inganta rayuwar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *