January 22, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Jami’ar Kwara ta rage wa masu buƙata ta musamman kuɗin karatu.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Jami’ar jihar Kwara da ke Najeriya ta sanar da rage naira 100,000 na kuɗin makaranta ga ɗalibai masu buƙata ta musamman.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Shaykh-Luqman Jimoh ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da muƙaddashin daraktar hulda da jami’ar, Dr. Saidat Aliyu ta fitar.

Hakazalika, ya ce jami’ar ta na aiwatar da tallafin naira 50,000 kowane wata ga ma’aikatan jami’ar masu fama da buƙata ta musamman tare da ƙarin guraben aikin yi ga masa a fannin koyarwa na masu buƙata ta musamman.

Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Kano sun tsunduma Yajin Aiki.

Kungiyar ASUU reshen jihar Bauchi ta shiga yajin aikin sai baba ta gani.

An yanke wa Jami’ar ABU Zariya lantarki saboda rashin biyan kuɗin wuta.

Jimoh ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a wani taron da aka shirya don bikin ranar masu buƙata ta musamman na duniya ta 2024 a ofishin tallafawa nakasassu na jami’ar da ke Sashen Ilimi na Musamman.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *