Labarai

Tubabbun Ƴan Boko Haram 6,900 Sun Koma Cikin Al’umma A Borno

gwamnati ba ta taba samun wani korafi dangane da wadanda aka dawo da su ba

Mayakan Boko Haram 6,900 daga cikin wadanda suka mika wuya ne suka dawo cikin al’umma a cewar Gwamnatin Jihar Borno.

Mashawarcin Gwamna Babagana Zulum na musamman kan harkokin tsaro, Janar Abdullah Sabi M. Ishaq (murabsu) ne ya bayyana hakan a yayin aikin tantance tubabbun ’yan ta’adda a Maiduguri.

Akalla mayakan Boko Haram 100,000 ne ya zuwa yanzu suka mika wuya bisa radin kansu, inda daga ciki aka tantance 6,900 aka kuma kawar da su daga mummunar akidar tasu.

Janar Abdullahi ya bayyana cewa an mayar da tubabbun ’yan Boko Haran 6,900 cikin kwanciyar hankali da iyalansu da kuma ’yan uwansu lafiya ne bayan tsare-tsare da aka yi da hadin gwiwar dukkanin masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin tsaro da hukumomin jin kai da ci gaban kasa daga gwamnatin jiha, kananan hukumomi, shugabannin addini da na al’umma da sauransu.

Ya kara da cewa kawo yanzu tubabbun mayakan Boko Haram 6,900 da aka dawo da su cikin al’ummarsu sun hada da kashi na farko 500, na biyu 1000, na uku 1000, na hudu 1000, na biyar 1,300 sai na shida 2,100, wanda jimilla 6,900 ne yayin da ana ci gaba da kaso na bakwai.

Janar Ishaq ya bayyana cewa gwamnati ba ta taba samun wani korafi dangane da wadanda aka dawo da su ba, “amma muna ta samun rahotanni da jinjina daga wasunsu cewa sun yi aure, wasu sun fara kananan sana’o’i, wasu kuma sun rungumi aikin noma kuma yana yin kyau matuka.

“Wannan abin yabawa ne ga hukumomin tsaro da gwamnatin jiha da kuma sarakunan gargajiya da kungiyoyin jinkai da ci gaban da ba don goyon bayansu da kokarinsu da taimakonsu da fahimtarsu ba, da ba mu kai inda muke a yau ba.

Ya ci gaba da cewa, sama da kashi 90 cikin 100 na masu tsaurin ra’ayi sun mutu ne sakamakon hare-haren soji, kuma kashi 85% na wadanda suka mika wuya matasa ne da aka tilasta musu shiga ayyukan ta’addanci.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button