December 26, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Allah ya yi wa Sarkin Ningi Alhaji Yanusa Ɗanyaya rasuwa.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Rahotanni a jihar Bauchi da ke Najeriya na cewa, Allah ya yi wa mai martaba sarkin masarautar Ningi da ke jihar rasuwa Alhaji Yanusa Muhammad ɗanyayaa ranar Lahadi.

Da ya ke tabbatar da rasuwar cikin wani saƙo da aka yaɗa ta kafofin sada zumunta, sakataren fadar Ningi Alhaji Usman Sule Maga Yaƙin Ningi, ya ce Sarkin ya rasu ne a jihar Kano da Asubahin yau Lahadi.

Sarkin Ningi mai sharakara 88 an haife shi ne a 1,936 kuma an naɗa shi Sarkin Ningi ne a shekarar 1978 wato ya yi sharakara 46 ya na sarauta daga zuwa 1978 zuwa 2024.

Ana sa ran za a yi jana’izar Sarkin ne a fadar Sarkin Ningi da ke ƙaramar hukumar Ningi a jihar Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *