April 18, 2025

Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.

Gwamnatin Jihar Edo a ranar Juma’a ta rushe wani gida mallakin wani dattijo mai suna Karimu Audu, bisa zargin sa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.

An rushe gidan Audu da ke Eshioriri-Erah Karamar Hukumar Owan East, Edo ta Arewa, saboda zargin cewa ya na bayar da bayanai ga masu garkuwa da mutane.

Wannan rushewar na daga cikin yunkurin Gwamna Monday Okpebholo na kawar da ‘yan garkuwa, da sauran masu aikata laifuka a jihar.

Jihar ta ƙara matsa lamba a kan mutanen da ke taimaka wa ‘yan garkuwa, in da hukumar da ke yaki da masu aikata laifuka ta rushe wani gida da aka alakanta da ayyukan ta’addanci.

Baya ga zargin bayar da bayanai ga ‘yan garkuwa, ana kuma zargin Audu da ba su masauki da kuma ciyar da su.

Da yake magana da manema labarai a wurin, Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Tsaro Akhere Paul, ya jaddada cewa gwamnati ba za ta ƙyale duk wanda ke da hannu a garkuwa da mutane ba.

Ya ce, “Mun zo nan ne saboda hadin baki. Mutumin nan ya na aiki tare da ‘yan garkuwa a daji. Wannan ya zama izina ga kowa—idan ka ga wani abu, ka fada. Idan ka hada kai da ‘yan ta’adda, rana daya za ta zo maka kamar yadda ta zo wa wannan mutumin yau.”

Haka nan Kwamandan Rundunar Yaki da Ta’addanci ta Jihar Edo SP Michael Anetor, ya tabbatar da aniyar gwamnatin jihar na kawar da garkuwa da mutane gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *