Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Jam'iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha. - Martaba FM Jam'iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha. - Martaba FM

Jam’iyyar PDP ta yi waddai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawa ta yi, sakamakon zargin cin zarafin da yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, PDP a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta na Kasa Debo Ologunagba ya fitar, ta bayyana cewa matakin da shugabancin Majalisar Dattawa ya dauka kan Akpoti-Uduaghan ya na nuna yunkurin rufe gaskiya da hana adalci.

Jam’iyyar ta ce dakatar da Akpoti-Uduaghan cikin gaggawa ba tare da gudanar da bincike a kan zargin cin zarafin jima’i da ake yi wa Shugaban Majalisar Dattawa ba, ba wai kawai ya na cin zarafin dokokin sauraron korafi da ya kamata a yi a Majalisar ba, har ma yana nuna cewa Majalisar tana goyon bayan munanan dabi’u kuma tana kare masu aikata irin wadannan laifuka.

PDP ta bayyana cewa “dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shidda ba tare da adalci ba, yana nufin an hana mutanen yankin Kogi ta tsakkiya damar samun wakilci a Majalisar Dattawa, wanda hakan ya saba wa kundin tsarin mulki.”

Ta kara da cewa “abin kunya ne kuma babban cin zarafi ne ga adalci da dokokin sauraron korafi yadda Sanata Akpabio ke zama alkalin shari’a a kan lamarin da ake zargin sa da aikatawa. Wannan yana kara tabbatar da shakkun jama’a cewa Shugaban Majalisar Dattawa na kokarin hana bincike a kan zargin cin zarafin da ake yi masa.”

PDP ta tuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da ake zargin Sanata Akpabio da cin zarafi ta hanyar jima’i ba.

“Wannan lamari da ke faruwa a Majalisa yana tunatar da ‘yan Najeriya, yadda tsohuwar Mukaddashiyar Manajar Daraktan Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Dr Joi Nunieh, ta taba yin zargin irin wannan kan Akpabio.”

“Idan har Akpabio ba shi da abin boyewa, abin da ‘yan Najeriya suka yi tsammani shi ne ya sauka daga mukamin sa na wuccin gadi, kamar yadda tsarin Majalisa ya tanada domin bada damar gudanar da bincike mai zaman kansa da kuma wanke kansa daga zargin da ake yi masa.”

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *