Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Ma’aikatan rarraba wutar lantarki ta jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya ta yanke wa jami’ar ABU Zariya, wuta saboda ƙasa biyan kuɗin wuta da makarantar ta yi.
Cikin wata sanarwa da hukumar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta fitar, ta bayyana cewa ma’aikatan lantarki ta jihar Kaduna sun katse layin lantarkin da ya kai wa jami’ar wuta.
Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya akan kuɗin wutar da jami’ar ke sha a kowane wata, duk da cewa jami’ar ta yi iƙirarin biyan kuɗin wuta na sama da Naira biliyan ɗaya a wannan shekarar.
ASUU ta nuna damuwa kan yawaitar ɗaliban da ke samun sakamakon first-class a Najeriya.
Sama da ɗalibai dubu 12 ne suka zana jarrabawar neman shiga Jami’ar Yusuf Maitama da ke Kano.
NAHCON ta ce kowanne alhajin 2023 za a mayar masa da naira 60,080.
A baya-bayan nan ne dai aka bayyana Jami’ar ABU a matsayin jami’ar da ta fi kowace jami’ar gwamnati fice a Najeriya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.