Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun tsaikon samar da mai daga matatar mai ta Fatakwal, bisa dalilan da ba a bayyana ba.
A halin da ake ciki dai matatar Dangote na fama da cunkoson manyan motoci, lamarin da ke kawo tsaikon dakon man, amma IPMAN ta tabbatar da hakan ba zai haifar da ƙarancin man fetur a ƙasar ba.
Sai dai IPMAN ta yi kira ga gwamnati da ta sake duba farashin man fetur wanda tace ya haura naira dubu ɗaya kan kowace lita.
Ƙungiyar Limamai A Najeriya Na Son Gwamnati Ta Gyara Matatun Mai Na Ƙasar.
Zancen Man Fetur Ya Sauka Zai Yi Wahala, -Ɗangote.
Ƴan Kasuwar Man Fetur Sun Fara Siyen Man Daga Matatar Dangote.
A cewar Alhaji Salisu Ten-Ten, ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an shawo kan lamarin, kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da BBC.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP