January 3, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Ayyana Ƙasar Masar A Matsayin Wadda Ta Kawar Da Sauro.

Daga Umar Rabiu Inuwa

Nasarar Masar ta samu ta biyo bayan aikin kusan shekaru 100 da gwamnatin ƙasar da kuma al’ummatar ta su ka yi na kawo karshen cutar zazzaɓin cizon Sauro, acewar wata sanarwa da hukumar lafiya ta duniya ta fitar a jiya Lahadi.

Kasar Masar dai ita ce kasa ta uku da aka bai wa takardar shedar kubuta daga cutar zazzaɓin sauro a yankin gabashin Mediterrenean ta Hadaddiyar Daular Larabawa da Maroko, sai kuma ta farko tun shekara ta 2010.

punchng ta yawaita, a duniya baki ɗaya kasashe Arba’in da Huɗu (44) ne daga yanki daya suka kai wannan matsayin.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ba da takardar shedar kawar da cutar zazzabin cizon sauron ba tare da wata shakka ba ganin cewa dama an dakile yaduwar cutar zazzabin cizon sauro wadda sauro Anopheles ke kawo wa, a duk faɗin kasar tun shekaru ukun da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *