December 9, 2024

Na Dinke Barakar da a’ke samu yayin bikin Mauludi da Wakokin Yabon Fiyayyen Halilta – Sarkin Kasidun Bauchi

Daga Jibrin Hussaini Kundum, Bauchi

La’akari da yadda masu wakokin yabon Fiyayyen Halilta wato (Sha’irai) a jihar Bauchi keyi an samar da tartibiyar mafita gare su wanda zai alkinta wannan fanni na yabo domin tabbatar da haɗin kai tsakanin Al’ummar Musulmai.

Sarkin Kasidun Bauchi, Alh. Muhammad Tukur Mato ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai dangane da shirye-shiryen bikin cikar shi shekaru biyu (2) da samun sarautar Sarkin Kasidun Bauchi.

Ya bayyana cewar cikin shekaru biyu da suka gabata ya shirya taron kara wa juna sani wa Sha’irai dake jihar Bauchi domin sanin ire-iren kalamai da Mawakan zasu keyi yayin yabon fiyayyen halirta.

Alh. Muhammad Tukur ya gano cewar yaki da kalaman da basu dace wajen yabon Annabi (S.W.A) ko shakka babu suna kawo koma baya ga rayuwar al’umma,yana cewar dole suka tashi tsaye domin wayar da kai tare da sanya linzami ga Mawakan musamman Mawaka Mata a jihar.

Sarkin Kasidun Bauchi ya cigaba da cewar Gwamnatin Jihar Bauchi cikin shekarun da suka ga bata ta dauki nauyin gudanar da bikin Mauludin Fiyayyen Halilta tare da gudanar da addu’ah wa jihar Bauchi, a Gandun Dajin Yankari wanda hakan abun ya bawa ne.

Alh. Muhammad Tukur Mato yace cikin shekaru biyu bisa Sarautar Sarkin Kasidun Bauchi ya sami nasarori tare da lambobin yabo daga ciki da wajen Jihar Bauchi yana cewar hakan abun godiya ga ALLAH (S.W.A) ne matuka.

Ya kuma yi amfani da wannan damar Inda ya bukaci sauran Sha’irai a jihar Bauchi da sauran Jihohin Tarayyar Najeriya dasu kasance masu bin koyaswar addinin Islama tare da neman Ilimi ga banin rera baituka wa Shugaban Halilta Annabi (S.A.W)

Daga karshe ya mika godiyar shi ga Sarkin Bauchi Alh. Dr. Rilwanu Suleiman Adamu bisa mara mishi baya tare da nuna kauna ga sha’anin yabon Annabi (S.A.W)

Yace Maimartaba Sarkin Bauchi ya chan chan ci yabo bisa tabbatar mishi da wannan sarauta mai albarka, shekaru biyu da suka shude.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *