Sojojin Runduna ta ɗaya karkashin shirin Operation Fansar Yamma, sun samu gagarumar nasara wajen rage ayukkan ‘yan ta’adda a jihohin Kebbi da Zamfara.
Kwamandan Runduna ta ɗaya ta Sojojin Najeriya dake Gusau, Birgediya Janar Timothy Opurum ne ya bayyana hakan yayin liyafar Sallah da aka shirya tare ga jami’an sojoji da iyalan su a sansanin rundunar da ke Gusau a ranar Talata.
Janar Opurum ya bayyana cewa nasarorin da aka samu a kan ‘yan ta’addan, sun rage munanan ayyukan su a yankunan da ke karkashin kulawar rundunar.
Ya jaddada cewa a baya lamarin tsaro ya kasance mai matukar wahala, amma sojojin sun samu rinjaye a yankin kuma sun dakile ayyukan ‘yan ta’adda, ta hanyar jajircewa da cigaba da gudanar da hare-hare na soja.
“Runduna ta 1 tana kokari sosai a ayyukan ta, musamman a cikin Operation Forest Sanity III da ake gudanarwa. Idan za a iya tunawa, watanni kadan da suka wuce lamarin bai kasance mai sauki ba, amma da kokarin sojojin mu da manyan jami’an mu, mun samu damar mamaye yankin da ke karkashin mu kuma mun ragargaza ‘yan ta’adda matuka,” in ji Opurum.
Ya yaba wa sojojin bisa sadaukarwa da jajircewar su, inda ya bayyana cewa a sakamakon wannan kokari, Babban Hafsan Sojojin Kasa Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya amince da samar da karin kayayyakin aiki domin inganta ayyukan su.
Kwamandan yayin da yake jinjinawa sojojin kan kokarin su, ya kuma bukace su da su ci gaba da jajircewa da nuna himma don tabbatar da cewa an samar da tsaro a dukkan jihohin Arewa maso Yamma domin zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.
Ya ce “Dole ne mu ci gaba da yaki har sai mun murkushe dukkan abokan gaba, kuma mu tabbatar da cewa Zamfara, Kebbi da sauran jihohin da ke cikin wannan yanki sun zama wuraren da suka kasance cikin aminci da tsaro, domin ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
“Sakamakon nasarorin da muka samu, Babban Hafsan Sojojin Kasa ya amince da karin kayayyakin aiki domin ci gaba da ayyukan mu. Wannan yana nufin cewa wanda aka ba dama mai girma, ana sa ran kokari daga gare shi. Don haka, dole ne mu ninka kokarin mu, domin ba a kai ga nasara gaba daya ba, har yanzu akwai aiki mai yawa a gaban mu,” in ji Opurum.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP