January 22, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

“Yawancin maganganun da ake yi na suka a kan ƙudurin ba ana yin su ne bisa wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, illa shaci faɗi kawai”-Tinubu.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Fadar shugaban Najeriya ta ce babu wani sashe na sabon ƙudurin haraji da ta gabatar ga majalisa domin samun amincewa da ya tanadi soke wasu hukumomi irin su TETFUND, da NASENI, da kuma NITDA.

Haka kuma ta ce ƙudurin kamar yadda ake ta yaɗa maganganu ko alama ba zai jefa yankin Arewacin ƙasar cikin talauci ba.

BBC ta rawaito, mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya bayyaa haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.

Ya ce yawancin maganganun da ake yi na suka a kan ƙudurin ba ana yin su ne bisa wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, illa shaci faɗi kawai.

Majalisar dokokin jihar Kano ta nuna rashin amincewa da sabuwar dokar haraji wadda gwamnatin Najeriya ke son aiwatar wa.

“Bai kamata tsare- tsaren kuɗi da gwamnati ke son ingantawa ya fifita wasu jihohi ƙalilan ta hanyar ruguza sauran ba”- Atiku Abubakar.

Gwamnan Kano ya gana da ƴan majalisar wakilai na Kano Kano sabuwar dokar haraji.

Onanuga ƙara da cewa, ya yayin da wasu masu sharhin suka yi ƙoƙarin haifar da saɓani tsakanin jama’a da ‘yan majalisar dokoki, wasu kuma sun raba kan ƙasar ne tsakanin wani sashe da wani.

Kakakin ya ce ko alama wannan ƙuduri ba zai azurta jihar Lagos ko Ribas, ya kuma sa wasu sassan ƙasar su ƙara talaucewa ba kamar yadda ake yayatawa ba.

Ya ce saɓanin wannan zargin ƙudurin zai taimaka ne wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya, musamman ma masu ƙaramin ƙarfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *