January 22, 2025

Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Gwamnatin tarayya ta bayyana za ta ci gaba da aikin gyaran manyan madatsun ruwan Kano ta Kudu da suka hadar da dam din Challawa na Karaye, da na Tiga da ke Bebeji, da kuma na Kafin Ciri da ke karamar hukumar Garko.

hahotanni sun tabbatar da cewa Babbar Sakatariya mai kula da hukumar kare muhalli ta kasa, a ofishin sakataren Gwamnatin tarayya, Dr. Aishetu Gogo ce ta bayyana hakan, yayin da ta jagoranci masana muhalli da masu ruwa da tsaki daga Gwamnatin tarayya suka ziyarci wuraren.

Gogo ta ce, tuni gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta fara shirin gyaran dam din Challawa Goje, da na Tiga da kuma na Kafinchiri a yunkurin tabbatar da inganta harkokin manoma, da kuma ganin manoman yankin sun amfana da su don wadata kasa da abinci da bunkasa tattalin arzikin Nigeria.

Yunkurin ci gaba da aikin na zuwa ne, bayan Sanatan Kano ta kudu Abdurrahman Kawu Sumaila da wasu masu ruwa da tsaki a jihar Kano, suka bukaci shugaba Tinubu da ya karasa aikin domin amfanin da al’ummar yankin dama kasa baki daya.

Da take ganawa da manema Labarai jim kadan bayan kammala zagayen madatsun ruwan, Dr. Aishetu Gogo, ta bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki a jihar Kano domin samun nasarar aikin.

Ta kuma ce gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta dauki matakin gyaran madatsun ruwan ne, domin kaucewa abin da ya faru a birnin Maiduguri na jihar Borno, na iftila’in ambaliyar ruwa sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau.

Gogo, ta kara da cewa ofishin ta mai na kula da muhalli na kasa, na kokarin magance duk wasu matsaloli da suka shafi jihohin kasar nan 36 har da Abuja, a yunkurin magance matsalolin gurbacewar muhalli da ambaliyar ruwa.

Wasu manoman da aka ziyarci yankunansu, aganawar su da wakiliyarmu sun bayyana cewa, “kammala aikin zai kara bunkasa harkokin noma da suke gudanarwa.
Sun kuma bukaci mahukunta da su yi abin da ya dace, wajen cika alkawarin da suka dauka na kammala aikin cikin kankanin lokaci.”

A nasa jawabin Sanatan Kano ta kudu Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce,” rashin kammala aikin na daga cikin abin da yake ciwa mazauna Kano ta kudu tuwo akwarya”.

Sai dai ya mika jinjina ga Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya ji kokensu kuma ya bukaci a ci gaba da aikin.

Kawu Sumaila, wanda ya samu wakilicin Aliyu Abubakar Bullet, ya ce dama yankin Kano ta Kudu noma yana daga cikin abin da suka dogara da shi.

Har ma ya bayyana idan aka kammala aikin gyaran manyan madatsun ruwan, harkokin noma za su inganta matuka, wanda hakan zai farfado da tattalin arzikin yankin dama jihar Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *