Kano

Labarai

Samar Da Aikin Yi Ga Matasa Ka Iya Rage Matsalar Rashin Tsaro- Sarkin Kano.

Daga Muhammad Sadik Umar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero,  ya ce samarwa matasa aikin yi zai iya taimaka wajen rage matsalar rashin tsaro a jihar Kano dama Najeriya baki daya. Sarkin  Kano, ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakƙuncin shugabanin cibiyar Koyan Zayyanar Sadarwa IGC, ƙarkashin jagorancin Dakta Ibrahim Garba […]

Read More
Labarai

Kano: Rundunar Yan Sanda Ta Gargaɗi Mazauna Jihar Da Ke Yaɗa Labaran Ƙarya Kan Tsaro.

  Da take kore raɗe-raɗin ganin wasu da akai zargin ƴan ta’adda ne da suka kai su kimanin su ɗari bisa babura a wata unguwa mai suna Kuntau da ke Kano, rundunar ƴan sandan jihar ta gargadi masu yaɗa labaran ƙarya kan abinda ya shafi tsaro da ahir ɗin su. Tana mai cewa tsaro muhimmin […]

Read More
Siyasa

Zaɓen 2023: Za Mu Tabbatar An Gudanar Da Sahihin Zaɓe A Jihar Kano- Ganduje.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa al’ummar jihar Kano tabbacin cewa za a gudanar da sahihin zabe a zaben shekarar 2023 mai zuwa. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC da suka shirya gangami domin nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na […]

Read More
Labarai

An Naɗa Ganduje Ne Sarautar “Olorogun Ejerukugbe” A Ranar Asabar.

An sake naɗa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da mai ɗakinsa sabuwar sarauta, a masarautar Olomu dake jihar Delta. An naɗa Ganduje a matsayin ‘Olorogun Ejerukugbe’ wadda ke nufin ‘aiki tare’, sannan mai ɗakinsa Hafsat Ganduje a matsayin ‘Olorogun Omarmoraye’, wato ‘Mutuniyar kirki’ a harshen Hausa. Sarkin Olomu, Ovie Dr R.L Ogbon, Ogoni, Oghoro 1 […]

Read More
Tsaro

Kano: Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jawo Rasa Ran Mutum Guda Da Jikkata Wasu Biyar – Ƴan Sanda.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya inda kuma biyar suka jikkata sakamakon rikicin Manoma Da Makiyaya da ya afku a garin Kuka Bakwai, da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar. Rundunar yan sandan ta ce an samu ɓarkewar  rikicin ne […]

Read More
Ra'ayi

Me Ya Sa Aurenmu Ya Ke Yawan Mutuwa?

Mun dan yi wani bincike da mu ka gano wasu abubuwan da ke saurin kashe aure ko da maaurata suna son junansu, za mu fara dauko su daya bayan daya muna tattaunawa. Abu na farko da ke cikin wannan rukunan da ke kawo matsaloli a zamantakewar auranmu (hausawa) har ya kai ga rabuwa shine rashin […]

Read More
Siyasa

Gwamnatin Kano Na Zargin NNPP Da Kai Wa Al’umma Harin Da Ya Yi Sanadin Rasa Rai Da Kwace Wayoyin Al’umma.

Daga Sadik Muhammad Umar Gwamnatin jihar Kano karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta yi Allah-wadai da harin da ta yi zargin jam’iyyar NNPP ta kaiwa mazauna gari, wanda ta ce  har an  sace wayoyin hannun mutane. Gwamnatin ta bayyana hakan ne da kakkausar murya kan ta’asar da ta ce  ƴaƴan jam’iyyar  NNPP suka yi a jihar […]

Read More
Labarai

Kano: Sa’insa Ta Jawo Rasa Ran Wani  Matashi.

Daga  Umar R Inuwa Rundunar jihar Kano ta tabbatar da rasa ran wani matashi Ibrahim Khalil Usman,  mai kimanin shekara 16 a unguwar Ƙofar Mazugal bayan da sa’insa ta barke tsakanin sa da wani abokin sa. Matasan, mazauna ƙofar Mazugal, da ke ƙwaryar birnin kano, Saminu Bala ɗan kimanin shekara 18 da Ibrahim Khalil Usman […]

Read More
Labarai

Ƴan Sanda Na Bincike Kan Masu Hawan Dokin Da Kashe Matashi A Kano.

Daga Umar R Inuwa A jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ana zargin wasu mahaya Dawaki domin yin kilisa da kashe wani yaro mai suna Abdulhadi Sammani, mai shekaru 20, ɗan unguwar Sani Mai Nagge. Ana zargin kimaninn mahaya dawaki 40 ne suka yi fitar ɗango a ranar Lahadin da ta gabata, Inda suka dunga […]

Read More
Ra'ayi

Rashin Ƙarfafawa Ke Durƙusar Da Masu Fasahar Mu A Najeriya Musamman Ƴan Arewa.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Allah ya azurta ƴan Arewa da mutane iri-iri da suke da baiwar ƙirƙire-ƙirƙire da ƙere-ƙere da yawan gaske kuma a kowane sako da lungu na ƙasar nan musamman ma a wannan yanki namu na Arewa, to amma basa samun cigaba. Suna rasa cigaba ne saboda rashin ƙarfafawa daga gwamnatoci, mawadata da […]

Read More