December 2, 2021

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ƙadiriyya Social Media Zata Koyar Da Matasa Sana’o’in Hannu.

Page Visited: 177
0 0
Read Time:1 Minute, 9 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya na Afrika Sheikh Abdulkadir Ƙariballahi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara ya jinjinawa ayyukan Darul Qadiriyya Social Media da suka yi na fitar da labarai a lokutan tarukan maukibin Ƙadiriyya karo na 71.

Sheikh Abdulkadir Qariballahi ya ce, Darul Qadiriyya Social tayi kokari sosai “mun gode Allah ya saka muku da alkairi.

Kazalika yayi kira ga Darul Qadiriyya Social Media su kara dagewa domin ganin sun ciyar da addini musulunci gaba dama ɗariƙar Ƙadiriyya.

Hakan na zuwa yayin wata liyafar cin abinci da ya shirya musu da da nufin ban gajiya da godiya tare da wasu kwamitoci da suka yi aiki tukuru domin ganin taron yayi nasara.

Da yake zantawa da Martaba FM jin kaɗan bayan tashi daga liyafar Malam Nura Abba Maimuƙami shugaban Darul Qadiriyya Social ya ce, shakka babu wannan liyafar ta kara musu azama tare da sa su dole su kara zare kansakali domin cigaba da bayar da kariya addinin musulunci da kuma yada shi.

Nura Abba ya ce, nan gaba akwai shirye-shirye da za su bijiro da su na koyar da matasa sana’o’in hannu domin su dogara da kansu da kaucewa zaman banza.

A ranar asabar din da ta gabata ne dai mabiya darikar Qadiriyya a duniya suka yi taron murnar haihuwar shehin su Sheikh Abdulkadir Jilany a fadin duniya, inda a Najeriya Sheikh Abdulkadir Qariballahi ya jagoranci taron karo na 71.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *