Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Mayan hare-haren da India ta soma kai wa muhimman wurare a Pakistan - Martaba FM Mayan hare-haren da India ta soma kai wa muhimman wurare a Pakistan - Martaba FM

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Alaƙar India da Pakistan ta kara kazancewa bayan da sojojin India suka kai hare-hare kan wasu wurare a yankin Pakistan-administered Kashmir da jihar Punjab ta gabas, a matsayin ramuwar gayya ga harin da aka kai kan yawon bude ido a Kashmir, wanda New Delhi ke zargin Pakistan da hannu a ciki – zargin da Islamabad ta musanta.

A safiyar Talata, karar fashe-fashe da dama ta karade birnin Muzaffarabad, hedikwatar yankin Kashmir da ke hannun Pakistan, kamar yadda rahoton Reuters ya bayyana.

Hukumomin tsaro guda uku a Pakistan da kamfanin labarai na Associated Press sun tabbatar da cewa makamai sun auna wurare a Kashmir da ke karkashin Pakistan da kuma lardin Punjab.

Gwamnatin India ta bayyana cewa hare-haren nata sun mayar da hankali ne kan “tushen ‘yan ta’adda a Pakistan da yankin Jammu da Kashmir da Pakistan ke rike da su, wadanda daga nan ne ake shiryawa da jagorantar hare-hare kan India.”

Ta kara da cewa: “Matakan da muka dauka sun kasance masu takaituwa, na hankali, kuma ba su da nufin tayar da hankali ko fadada rikici. Babu wata cibiyar soja ta Pakistan da aka kai wa hari. India ta nuna juriya sosai wajen zabar wuraren da aka kai hari da kuma yadda aka aiwatar da su.”

Sai dai rundunar sojin Pakistan ta ce hare-haren na India sun kashe mutane biyu tare da jikkata 12.

Wani kakakin sojin Pakistan ya bayyana wa gidan talabijin na Geo cewa an kai hari a kalla wurare biyar – ciki har da masallatai biyu – ya na mai cewa Pakistan na kan daukar matakin mayar da martani, ko da yake bai fadi takamaiman matakin da za su dauka ba.

Wannan sabon ci gaba ya zo ne bayan harin da aka kai wa matafiya a Kashmir da India ke rike da shi, wanda ya haifar da zazzafar musayar kalamai tsakanin manyan kasashen nukiliya biyu.

A baya, irin wadannan hare-hare sun haifar da barazana ga zaman lafiya a yankin Kudancin Asiya, wanda ke fama da rikici kan yankin Kashmir tun bayan samun ‘yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1947.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *