January 19, 2022

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ƴan Fashin Daji Sun Tashi Wani Gari A Jihar Zamfara.

Page Visited: 1617
0 0
Read Time:58 Second

Rahotanni daga jihar Zamfara, na cewa Gomman mutane sun tsere daga ƙauyen ‘Yan Ɓuki cikin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, bayan wani harin ‘yan fashin daji ya yi sanadin hallaka mutum bakwai.

BBC Hausa ta rawaito cewa, wani mazaunin ƙauyen da shi ma ya tsere zuwa Gusau ya ce da misalin karfe 12 na rana ne maharan suka shigo garin, tare da bude wuta, sun kuma shiga gidaje suna fito da mata da kananan yara da maza har da tsofaffi sama da 50, suka yi cikin daji da su, sannan sun ƙone musu dukiyar da ba a san adadinta ba.

Mutumin ya ce su ma Allah ne ya kubutar da su, suka samu tserewa tare da shiga motar da ta kai su birnin Gusau, ”bayan mutanen da suka tafi da su, sun kuma kashe mutum bakwai, ciki har da dan uwana uwa daya uba daya mai suna Abdullahi.”

“Har cikin daki suka shiga suka fito da shi, yana turjewa amma haka suka harbe shi a baya da kuma makoshinsa,” in ji mutumin da bai so a bayyana sunansa ba.

Sai dai kawo yanzu ‘Yan sanda ba su tabbatar da wannan harin ba.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *