Ƴan sanda a Zamfara sun ceto mata shida da jariri ɗan shekara ɗaya da aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a garin Gusau a yau Lahadi, inda ya ce masu garkuwa da mutane sun kama mutanen ne a kauyen Kadamutsa da ke karamar hukumar Zurmi a ranar 24 ga watan Nuwamba.
Sai dai ƴan sanda sun ceto mutanen bakwai a hanyar Zurmi zuwa Jibia a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba.
Mista Shehu, mai muƙamin Sufeto, ya ƙara da cewa, an yi nasarar ceto mutanen ne tare da taimakon kungiyoyin sa-kai na yankin da kuma rahoton sirri da ƴan sanda su ka samu.
“Jami’an ‘yan sanda sun je yankin da aka gudanar da aikin ceto waɗanda aka yi garkuwar da su a kan babbar hanyar Zurmi zuwa Jibiya inda aka ceto duk wadanda abin ya shafa ba tare da wani rauni ba.
“An kai wadanda aka ceto zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu, ‘yan sanda sun yi bayaninsu sannan aka mayar da su ga iyalansu,” in ji Mista Shehu.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, Kolo Yusuf ya yabawa jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga bisa nasarar ceto su.
M Yusuf ya kuma taya wadanda lamarin ya shafa murnar samun ‘yancinsu, ya kuma jaddada aniyar ‘yan sanda na ci gaba da kawar da miyagun laifuka a jihar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Gargadi Mazauna Jihar Kan Atisayen Harbin Bindiga A Kalebawa.
-
Ba Zamu Lamunci Daba Da Shaye-Shaye A Unguwarmu Ba- Al`Ummar Dala.
-
Ayyukan Laifin Da Aka Aikata A Kano Cikin Shekarar 2022 Sun Ragu Fiye Da 2021- Ƴan Sanda.
-
Jami’an Tsaro Sun Hallaka Ƴan Bidinga Tare Da Ragargaza Maɓoyarsu.
-
TSARO: Gwamnatin Buni ta na ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya don tunkarar matsalolin tsaro a Yobe